Shugaban Hukumar kwallon kafa na Sifen Jabier Tebas ya bayyana cewa sun dauki tsauraran matakan tsaro a kokarin ganin an yi wasa a tsakanin Real Madrid da FC Barcelona a gobe Asabar ba tare da an samu wata matsala ba.
daukar wannan mataki ya biyo bayan harin bama-bamai da wadansu ’yan ta’adda suka kai birnin Paris na Faransa a ranar Juma’ar da ta wuce. Hakan ta sa aka soke wasannin sada zumunta da Jamus ta shirya yi da Holland yayin da aka soke wanda Sifen ta yi niyyar yi da Beljiyam.
“Sifen tana daya daga cikin kasashen da ’yan ta’adda suke neman kai wa hari, don haka ne hukumar shirya kwallon kafa ta dauki kwararan matakai,” inji shi.
“Kowace kasa musamman a Nahiyar Turai sun shiga taitayinsu game da matsalar tsaro, don haka ne Sifen ta dauki wannan mataki a wasan Madrid da na Barcelona.
Shugaban ya ce za a tsaurara matakan tsaro ne a ciki da kuma wajen filin wasan Madrid don ganin ’yan ta’adda ba su maimaita abin da ya faru a Faransa ba.
Dubban jami’an tsaro ne ake sa ran za su kewaye harabar filin da kuma cikin filin don samar da tsaro a lokacin da wasan ke gudana.