✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mun tara kudin shiga na N2.3trn a bana —Hukumar Kwastam

Adadin ya zarta Naira tiriliyan 1.687 da aka yi hasashen hukumar za ta tara a bana.

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta sanar da samun nasarar tara fiye da Naira tiriliyan 2.3 a matsayin kudaden shiga ga Gwamnatin Tarayya daga watan Janairu zuwa ranar 19 ga watan Disamba na bana.

Mataimakin Babban Jami’in Hulda da Al’umma na Hukumar Kwastam, Timi Bomodi ne ya bayyana hakan ranar Litinin yayin wani taron masu ruwa da tsaki da Hukumar ta gudanar tare da manema labarai a shiyyarta ta Apapa da ke birnin Ikkon Legas.

Bomodi ya ce wannan kudaden shiga da hukumar ta tara ya zarta adadin Naira tiriliyan 1.687 da aka yi hasashen za ta tara a bana na.

Haka kuma, ya bayyana cewa shiyyar Apapa da kuma ta tashar ruwa da ke Tin-Can su ne ofisoshi biyu da suka tara kaso mafi tsoka na kudaden shigar da aka samu.

A cewarsa, “ina so na tabbatar muku da cewa a yanzu mun tara sama da Naira tiriliyan 2.3 na kudaden shiga a bana, wanda ya zarta adadin Naira tiriliyan 1.687 da aka yi hasashen za mu tara a wannan shekara.”

Hakazalika, ana sa ran za mu ci gaba da samun nasarori doriya a kan wadanda aka samu wajen rufe iyakokin kasar domin dakile safarar haramtattun kayayyaki, kananan makamai da fasa kwauri da sauran laifuffuka na kan iyaka.

%d bloggers like this: