Gwamnatin Yobe ta sanar da soke lasisin duk makarantu masu zaman kansu da ke jihar, tana mai kiran masu makarantun su bi tsarin da gwamnati ta shinfiɗa don neman sabon lasisi.
Kwamishinan ilimi na jihar Dakta Muhammad Sani Idriss, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, a ganawar da suka yi da masu makarantu masu zaman kansun, a makarantar sakandaren Gwamnatin Tarayya ta GGC Damaturu.
- ‘A kula da tubabbun ’yan kalare kamar yadda ake kula da tubabbun ’yan Boko Haram’
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 7 ’yan gida ɗaya a Abuja
Kwamishinan ya bayyana cewa daga yanzu duk wasu lamura na makarantun za su riƙa tafiya kafaɗa-da-kafaɗa da makarantun gwamnati, ba za a ƙara ba su damar gaban kansu ta fuskar dokoki da sauransu ba.
A jawabin da ya yi wa mahalarta taron, Dokta Muhammad Sani Idriss ya ce gwamnatin ta ɗauki matakin samun cikakken iko kan harkar ilimi a jihar tare da nuna rashin amincewa da manufofin wasu makarantu masu zaman kansu wanda ya ce ya saba wa ka’idoji da dabi’u na al’ummar jihar.
Ya ƙara da cewa babu wata makaranta da za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta ba tare da sabon lasisi da bin dokar da gwamnatin Jihar Yobe ta gindaya ba.
Ya ce, “Mun soke lasisin makarantu masu zaman kansu, don haka za su sake sabo.
“Sannan a lura, babu wata makaranta mai zaman kanta da muka rufe, amma abin da muke cewa shi ne, duk wata makaranta mai zaman kanta da ba ta da lasisi daga yanzu ba ta shirya ci gaba da gudanar da harkokinta ba.
“A baya an ba su wannan damar kai tsaye, amma an bukaci su bi wasu dokoki amma hakan bai samu ba, shi ya sa muka ɗauki wannan matakin.”
Da yake jawabi, shugaban Kwamitin Ilimi na Majalisar Dokokin Jihar Yobe mai wakiltar mazabar Damagum, Alhaji Maina Digma Gana, ya ce taron ya zo ne a lokacin da ya dace.
Ya ba da tabbacin cewa majalisar jihar za ta goyi bayan duk wani yunkuri na samar da ingantaccen ilimi ga al’umma.
A nasu bangaren, wasu daga cikin masu makarantun da suka zanta da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, sun ce taron ya zo a ne a kan gaba.
Sai dai sun shawarci gwamnatin da ta sauƙaƙa tsarin bayar da lasisin, wanda za su samu ba tare da ɗaukar wani dogon lokaci ba.