Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke hawan sallah na bana ne bisa shawarwari dangane da tsaro da aka bayar domin wanzar da zaman lafiya a jihar.
Sarkin ya faɗi hakan ne cikin wani saƙon taya murna da barka da sallah da ya yi wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Ya yi waɗannan kalamai ne a wani shiri na kai-tsaye da aka yaɗa daga ƙaramar fadar Nassarawa da ke jihar, a ranar Asabar.
Ya ce, “A wannan rana ta Arafat, muna miƙa saƙon barka da sallah ga ɗaukacin al’ummar Musulmi a wannan lokaci mai muhimmanci.
“Idi lokaci ne da Annabinmu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya koyar da mu yin layya da dabbobi idan za mu iya, waɗanda ba za su iya ba, muna roƙon Allah Ya buɗa su.
“Muna miƙa sakon fatan alheri ga Shugaban ƙasa da Gwamna game da zagayowar sallah tare da addu’ar Allah Ya ba su ikon yin shugabanci na gari.
“Muna kira a gare su da su ci gaba da samar wa al’umma ribar dimokuraɗiyya, tare da kare rayuka da dukiyoyinsu, muna kuma roƙon jama’a da su yi wa shugabanninsu addu’a.
“Mun soke duk wani shiri game da hawan sallah bisa shawarar jami’an tsaro don tabbatar da zaman lafiya.”
A halin da ake ciki, Sarkin Dawaki, Aminu Babba Ɗan Agundi, ya bayyana cewa Sarkin zai yi Sallar Idi a ƙaramar fadar Nassarawa, a ranar Lahadi da misalin ƙarfe 8 na safe.