✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mun shirya tsaf domin sake bude makarantu —Gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta shirya tsaf domin sake bude makarantu a jihar. Kwamishinan Ilimi, Muhammad Sanusi Sa’id ya bayyana hakan yayin bude wani…

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta shirya tsaf domin sake bude makarantu a jihar.

Kwamishinan Ilimi, Muhammad Sanusi Sa’id ya bayyana hakan yayin bude wani taron bita da aka shirya wa shugabannin makarantun firamare da sakandare a jihar kan matakan kariya daga cutar COVID-19 a Kano ranar Talata.

“Wannan taron ya zama wajibi kasancewar mun fara shirin bude makarantu kamar yadda Kwamitin Kar-ta-kwana da shugaban kasa ya kafa kan yaki da cutar ya umarta.

“Tuni muka yi wa makarantu 538 feshin magani, ciki har da masu zaman kansu; babu wata jiha da ta yi makamancin wannan hobbasan a duk Najeriya”, inji Kwamishinan.

Ya kuma ce jihar ta hanyar ma’aikatarsa ta samar da dukkannin kayayyakin kariya da ake bukata a makarantun lokacin da aka fara bude su a shirye-shiryen rubuta jarabawar WAEC ga dalibai masu kammala sakandare.

Kazalika, kwamishinan ya kuma ce gwamnatin jihar ta kashe sama da Naira biliyan hudu wajen ciyar da dalibai ‘yan makaranta a jihar da ma sauran bukatu.

Daga nan sai ya ja kunnen shugabannin makarantun kan su tabbatar suna ba daliban abinci mai inganci, inda ya ce zai rika kai ziyarar ba-zata don tabbatar da hakan.

“Idan har muka samu ana cin amanar gwamnati to lallai shugaban makarantar zai yaba wa aya zakinta”, inji shi.

Tun farko, shugaban Hukumar Kula da Makarantun Sakandire ta Jihar Kano (KSSSMB) Dokta Abdallah Shehu ya bayyana kwarin gwiwarsa kan sake bude makarantun inda ya ce tun farkon bude wasu daga cikinsu a makonnin da suka wuce domin rubuta jarrabawar WAEC ba a samu ko dalibi daya da ya kamu da cutar ba.

Ya ce an shirya horon ne ga shugabannin makarantun la’akari da muhimmancinsu wajen dorewar nasarar yaki da cutar da jihar ta samu.

Taron ba da horon na kwana hudu dai wanda ma’aikatun ilimi da na yada labarai suka shirya da hadin gwiwar kungiyoyi masu ba da tallafi ya tattaro shugabannin makarantu guda 50 daga sassan jihar domin ba su horo kan matakan kariya daga cutar COVID-19 da zarar an sake bude makarantu.