✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Kasashe sun ba mu N150m don zanga-zangar #EndSARS’

Kungiyar da ta jagoranci shirya zanga-zangar #EndSARS ta ce ta samu gudunmawar makudan kudade daga wasu kasashen waje da yawansu ya kai Dalar Amurka 400,000.…

Kungiyar da ta jagoranci shirya zanga-zangar #EndSARS ta ce ta samu gudunmawar makudan kudade daga wasu kasashen waje da yawansu ya kai Dalar Amurka 400,000.

Jimlar kudaden dai sun haura Naira miliyan 150 a kudin Najeriya.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadakar kungiyoyin karkashin Feminist Coalition suka fitar a shafukanta na sada zumunta a ranar Juma’a.

Kungiyar ta bayyana cewa ta tara gudummawar kudaden da ta samu daga sassan duniya daban-daban kuma har yanzu ba ta kammala kashe su ba.

Sai dai ta ce daga yanzu ba za ta sake karbar wata gudummawar kudi da sunan #EndSARS daga kowa ba.

Daga nan sai ta bukaci matasa da su bi dokar hana fita da aka saka a wasu jihohi a fadin kasar tare da kauce wa fakewa da zanga-zangar wajen tayar da zaune tsaye.