Hukumar EFCC mai yaki da masu yi tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, ta sanar da kwato dala miliyan 153 daga hannun tsohuwar Ministar Man Fetur, Diezani Alison-Madueke.
Shugaban Hukumar, Abdulrasheed Bawa wanda ya bayyana hakan dangane da rahoton ayyukan hukumar na watan Afrilu, ya kuma ce sun kwato akalla kadarori 80 a hannun tsohuwar Ministar wanda kudinsu ya kai dala miliyan 80.
- Sheikh Dahiru Bauchi ya gudanar da Idin karamar sallah
- Badakalar Naira Biliyan 165: PDP ta bukaci Buhari ya tsige Ministan Sufuri
Kwanaki kalilan gabanin karkare wa’adin mulkin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Diezani ta yi hijira inda ta koma Birtaniya da zama tun a watan Mayun shekarar 2015.
Sai dai kawo har yanzu hakar mahukuntan Najeriya bata cimma ruwa ba ganin an dawo da tsohuwar Ministar domin gurfanar da ita a gaban Kuliya kan zargin da ake mata na yin sama da fadi da wani kaso baitul-malin kasar.
A cewar Bawa, “Akwai abubuwa da dama da suka dabaibaye binciken da muke yi a kan Diezani, don na kasance daga cikin jami’an da aka dorawa alhakin bincikenta, kuma mun yi abubuwa da dama.
“A daya daga cikin binciken, mun gano dala miliyan 153, mun samu nasarar kwace kadarori sama da 80 a Najeriya wanda darajarsu ta kai kimanin dala miliyan 80.
“Sauran binciken da muke yi a kanta a halin yanzu sun shafi bayar da cin hancin dala miliyan 115 ga Hukumar Zabe ta Kasa INEC da yake gudana a fadin tarayya.
“Muna sa ran watakila nan da zuwa wani lokaci kadan za mu dawo da ita kasar nan sannan mu sake yin bitar lamarin don ganin matakin da za mu dauka nan gaba a kan lamarin.
“Amma tabbas har yanzu maganarta tana nan kuma ba mu yi watsi da batun ba don muna ci gaba da gudanar da bincike,” in ji Bawa.
Bawa y ace gurfanar da tsohuwar Ministar a gaban shari’a lamari ne da ba shi da cewa a kai kasancewar a halin yanzu tana wurin da Najeriya ba ta da wani iko a kansa.