Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa EFCC ta ce ta kammala shirye-shiryen kama wasu gwamnonin da wa’adin mulkinsu ke karewa wadanda ake zargi da ayyukan rashawa.
Hakazalika, EFCC din bayyana shirinta na kama wasu gurbatattun masu rike da mukaman gwamnati bayan mika mulki a ranar 29 ga watan Mayu.
- Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da zaben Ademola Adeleke
- Ramadan: An rage wa ma’aikata lokacin aiki a Jigawa
Shugaban EFCC, Mista Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka ranar Alhamis yayin tattaunawa da Aminiya.
Sai dai Bawa bai bayyana sunaye ko kuma yawan wadanda suke shirin kamawa ba da zarar sun suka daga kan mulki.
A sane cewa a bisa tanadin Kundin Tsarin Mulkin Najeriya dai, gwamnoni na cikin jami’an gwamnati da ke da kariya wadda ya hana a kama su idan suna kan mulki.
Shugaban na EFCC ya ce akwai ma’aikatun gwamnati guda biyu da hukumar ke bincike a kansu a halin yanzu saboda ayyuka da suka saba wa ka’ida da suke yi.
A cewarsa, a daya daga cikin ma’aikatun an yi almundahanar kudade ta N4bn na wasu kwangiloli kusan 20.
Bawa ya ce, “A yanzu haka, muna binciken ma’aikatu biyu da aka biya kudaden har sau biyu a cikinsu.
“Wadannan kwangiloli ne da aka yi tun shekarar 2018, sannan wasu mutane masu karfin hali suka fito da suka bayyana batun.
Ya ce an buga takardun bogi a cikin ma’aikatun, sannan da hadin-bakin wasu ma’aikata, aka kirkiri takardun karya tare da biyan kudi.
Bawa ya ce muddin aka mayar da harkokin gwamnati ta hanyar zamani, ba za a samu irin wadannan badakaloli ba.
Ya kuma mayar da martani kan wasu kungiyoyin farar hula da aka samu suna neman a kore shi, yana mai cewa hukumar ba za ta firgita ba ballantana hakan ya sa ta yi kasa a gwiwa.