✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mun kashe ’yan Boko Haram da ISWAP 31, mun kama 70 —DHQ

Dakarun kasar sun samu nasarar ceto mutum biyu da aka tsare.

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun kashe mayakan Boko Haram da kuma na ISWAP tare kuma da kama wasu 70 a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Hedkwatar Tsaron Najeriya DHQ ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da fitar a ranar Alhamis din nan kan nasarorin da sojijin kasar suka samu a makonni biyu da suka gabata.

Darektan Yada Labaru na DHQ, Manjo Janar Musa Danmadami ya bayyana cewa, mutum 70 daga cikin wadanda ta kama a yankin arewa maso gabas, 60 daga cikinsu sun kasance suna samar wa da ’yan tada-kayar bayan kayayyaki kamar abinci da makamai da man fetur da sauransu.

Danmadami ya ce dakarun kasar sun samu nasarar ceto mutum biyu da aka tsare, inda ’yan ta’addan 366 tare da iyalansu suka mika wuya.

Kazalika, Danmadami ya ce a ranar 11 ga watan Oktoba ne, sojoji suka yi wa ’yan ta’adda kwantan bauna a Bama da Ngala wanda ya kai ga mutuwar 18 daga cikinsu yayin da wasu suka tsere, inda aka kwato makamai da dama.

Manjo Janar Danmadami ya kuma ce cikin makaman da aka kwato sun hada da bindigar AK-47 guda biyar da bindigar M21 da buhunan wake 64 da na shinkafa biyar da magunguna da kayan sawa da kananan dabbobi da kudi naira 250,000 da babura 11 da kekuna biyar da sauransu.