Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, ta ce ta samu nasarar karasa dukkanin ayyukan da ta gada daga tsohuwar gwamnatin jihar da ta gabata.
Kwamishinan Ayyuka, Sufuri da Gidaje na jihar, Injiniya Tasi’u Dandagoro ne ya sanar da hakan yayin zanta wa da manema labarai cikin birnin Dikko.
- An fara binciken ayyukan gwamnati da suka yi kwantai
- Shekara 10 manyan ayyuka 114 sun gagara kammaluwa
Cikin wani rahoto da gidan Rediyon Freedom ya wallafa, Injiniya Dandagoro ya ce Gwamnatin jihar tana ci gaba da kashe makudan kudi wajen gudanar da ayyukan raya kasa da inganta rayuwar al’umma.
A cewarsa, “mun kashe biliyoyin nairori wajen samar da ayyukan ci gaba a jihar tare da kammala dukkan ayyukan da muka gada daga tsohuwar gwamnatin jihar da ta gabata.”