Mashawarcin Shugaban Kasa Kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya sanar da kama wasu ’yan siyasa da suka ba da gudunmawa Naira biliyan hudu domin gudanar da zanga-zangar yunwa.
Nuhu Ribadu ya ce an kama ’yan siyasan ne a Abuja da jihohin Kano, Kaduna da Katsina kan kasance daga cikin masu daukar nauyin zanga-zangar.
Ya sanar da hakan ne a yayin gabatar da rahoto ga taron Majalisar Kasa da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a Abuja.
Taron na ranar Talata ya samu halarcin tsofaffin shugabannin kasa irinsu Muhammadu Buhari, Goodluck Jonathan, Abdulsalam Abubakar da kuma Yakubu Gowon.
Jonathan da Buhari sun bayyana goyon baya da kwarin gwiwa cewa Gwamantin Tinubu za ta jagoranci Najeriya zuwa tudun mun tsira.
Taron shi ne na farko da Tinubu ya kira tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, kuma ya tattauna kan zanga-zangar da aka gudanar da matsalolin yunwa, tsaro da na tattalin arziki.
Majalisar Kasa ta ƙunshi Shugaban Kasa mai ci a matsayin shugabanta, sai mataimakinsa da tsofaffin shugabannin kasa da tsofaffin shugabannin alƙalan Najeriya.
Majalisar takan tattauna ne kan muhimman al’amuran da suka shafi kasa tare da lalubo hanyoyin magance su.
Sauran su e shugaban majalisar Dattawa da na majalisar wakilai da Antoni-Janar da sakataren gwamnatin tarayya da gwamnoni masu.