✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kama dilolin kwaya 352 a Kano – NDLEA

Hukumar ta yi kwacen ne a cikin wata uku

Hukumar Hana Sah da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta ce ta kwace tan 2.1 da kuma kama mutum 352 da take zargi da zama dilolin kwaya a Jihar Kano.

Kwamandan hukumar a Jihar, Abubakar Idris-Ahmad, ne ya bayyana hakan yayin wata zantarwarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Kano ranar Alhamis.

Ya ce an yi kamen ne daga watan Janairu zuwa Maris din da ya gabata.

A cewar Kwamandan, daga cikin mutanen, 208 maza ne, sai kuma mata 44, yayin da kwayoyin da aka kama sun hada da kilogiram 955.304 na tabar wiwi da kilogiram 1,225.05 na kodin da tramadol.

Sauran kwayoyin, a cewarsa, sun hada dagiram 25 na hodar Iblis, giram 52 na methamphetamine.

Sai dai Kwamwandan ya ce babban kalubalen da hukumar ke fuskanta a Jihar shi ne na shawo kan jama’ar gari su ba jami’anta bayanan sirri a kan masu ta’ammali da kwayoyin.

“Babban kalubalenmu a yanzu shi ne yadda mutane za su rika ba mu cikakkun bayanai a kan maboyar dilolin kwaya da harkokinsu, wadanda ke ci gaba da yin illa ga al’umma.

“Ya kamata mutane su yi takatsantsan da masu safarar kwayoyi da suke illata al’ummanmu don tabbatar da mun sami al’ummar da ba ta ta’ammali da kwayoyi,” in ji Kwamanda Abubakar. (NAN)