Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama kullin hodar iblis 105 a cikin kayan wani wanda ya dawo daga kasar Brazil a Babban Jirgin Sama na Murtala Mohammed da ke Legas.
Daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, ya sanar ranar Lahadi a Abuja cewa sun kama wanda ake zargin ne ranar Kirsimeti.
- Mutum 9 sun mutu a turmutsitsin murnar Sabuwar Shekara a Uganda
- Muhimman abubuwa a fagen kwallon kafa a 2022
Ya ce wanda ake zargin na daga cikin fasinjojin da suka dawo daga birnin Sao Paulo na kasar Brazil.
A cewarsa, bayanan sirrin da suka samu sun taimaka wajen kama wanda ake zargin a filin jirgin.
Ya ce, saura kiris ya sha sakamakon babu abin da suka gano a binciken farkon da suka yi masa.
Da aka tsananta bincike a kansa karo na biyu, sai aka gano hodar iblis din da yake dauke da ita, in ji jami’in.
Shugaban NDLEA na Kasa, Birgediya-Janar Buba Marwa (Murabus), ya sha nanata cewa ba za su raga wa masu fataucin miyagun kwayoyi ba ko’ina suke a fadin kasa.
(NAN)