Rasha ta yi ikirarin kakkabo jirage marasa matuka guda 42 da suka kai hari a yankin Crimea.
A safiyar Juma’a Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce 9 daga cikin jiragen an harbo su ne, sauran 33 kuma kashe su aka yi a sararin samaniya ta hanyar lalata manhajar da ke sarrafa su.
- Yadda ake jana’izar sojojin da ‘yan ta’adda suka kashe a Neja
- ISWAP da Boko Haram sun kashe wa juna mayaka 41
Kawo yanzu dai babu bayanin ko harin jirage ya yi barna a Crimea yankin da Rasha da mayar karkashin ikonta daga kasar Georgia a shekarar 2014.
Harin Crimea na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ta ke shirin horas da sojojin Ukraine kan tuki da kuma gyaran jiragen yaki samfurin F-16.
Kasar Norway ta yi wa Ukraine alkwarin gudummawar F-16, amma ba ta fayyace adadin ba, ko da yake ana kyautata zaton ba za su kai guda 10 ba.
A watan Oktoba ake sa ran Amurka za ta fara horas da sojojin na Ukraine a sansanint sojin sama na Tucson da ke yankin Arizona.