Shugaban Hukumar EFCC mai Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, Mista Abdulrasheed Bawa, ya zayyana yadda suka gano wata Minista a Najeriya da ta sayi kadarar wani banki ta kimanin dala miliyan 37.5 a boye.
Sai dai ba tare da bayyana sunan Ministar ko kuma Ma’aikatarta ballantana kuma gwamnatin da ta yi zamani ba, Mista Bawa ya ce tuni Matar ta biya zunzurutun tsabar kudi har dala miliyan 20 a matsayin kafin alkalami inda za take shirin cika ragowar daga baya.
Yayin wata hira da ya yi a shiri Sunrise Daily wanda gidan Talabijin na Channels ya saba daukar nauyi, Shugaban na EFCC ya ce tabbar ana ci gaba da yin sama da fadi da dukiyar al’ummar kasar nan ta hanyar sayen kadarori.
Ya ce masu halasta kudaden haramun a gwamnati na amfani da dabarar sayen kadarori musamman gine-gine domin boye kudaden da suka sata.
Ya bayyana lamarin dillancin gidaje da sauran gine-gine a matsayin hakar da a yanzu ta shahara wajen aikata barnar rashawa a kasar.
Ya ce, “Daya daga cikin matsalolin da muke fuskanta a kasar nan ita ce harkar gidaje, saboda kaso 90 cikin 100 na albarkatun kasar nan ana wawushe su ne ta hanyar harkar gine-gine.
“Bayan binciken da muka gudanar a kan lamarin wannan Minista, mun gano cewa Shugaban wani banki ne ya tallata wa Ministar wata kadara kuma ta amince za ta siya akan Dala miliyan 37.5.
“Daga nan ne bankin ya tura mota har gidan Ministar kuma ta kwaso zunzurutun tsabar kudi har Dala miliyan 20 a matsayin kafin alkalami, a cewar Bawa.