Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce an gano karin daliban makarantar sakandiren Kankara a jihar da aka sace tare da sada su iyayensu.
Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawar sa da Sashen Hausa na gidan rediyon kasar Jamus (DW) a ranar Litinin.
- Boko Haram ce ta yi garkuwa da daliban Kankara —Shekau
- GSSS Kankara: ’Yan bindiga sun tuntubi Gwamnatin Katsina
Gwamnan ya ce, “Ya zuwa Litinin, alkaluman da muka samu sun nuna cewa an gano 17 daga cikin daliban da aka sace.
“15 daga cikin su an gano su ne a kauyen Dinya da ke Karamar Hukumar Danmusa.
“Baturen ’yan sandan yankin ne ya shaida min hakan, mutum daya kuma a tsakanin yankin aka same shi, shi kuma dayan mahaifinsa ne ya kira ya tabbatar dan nasa ya dawo gida da kansa.
“Dukkan wadannan yaran tuni suka sadu da iyayen su tun da mun riga mun kulle makarantun.
“Akasarinsu na cikin dazuka a Jihar Zamfara, kuma muna iya bakin kokarinmu wajen ganin mun ceto dukkansu,” inji Masari.
Jawabin gwamnan na zuwa ne jim kadan bayan ya yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bayani a garin Daura kan irin fadi-tashin da jihar ke yi na ceto daliban da aka sace.
Sai dai a wani sabon sakon murya da kungiyar Boko Haram ta fitar, an jiyo shugabanta, Abubakar Shekau yana ikirarin cewa su ne suka sace daliban.