Sama da gidaje 200 ne suka lalace a ƙananan hukumomin Zariya da Sabon-Gari sakamakon ambaliyar ruwa a Jihar Kaduna.
Duk da hasashen ambaliyar da gargaɗin da aka yi, wasu mazauna sun ƙi yin ƙaura daga matsugunansu, wanda hakan ya janyo hasarar ɗimbin rayuka, Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (SEMA).
Babban Sakataren Hukumar ya ce “Bincikenmu ya gano muhimman batutuwa guda uku da suka haɗa: rashin isasshen tsarin magudanar ruwa, zubar da shara a magudanan ruwa da kuma gine-ginen da aka a cikin magudanan ruwa.
“Mun gabatar da sakamakon bincikenmu ga gwamnan, kuma ya umurci masu ruwa da tsaki da su fara aiki kan tsofaffin magudanan ruwa a faɗin jihar,” in ji shi.
- Lalube cikin duhu Gwamnatin Tinubu take yi —Atiku
- HOTUNA: ’Yan Shi’a da ’yan sanda suka kama bayan rikicin Abuja
A cewarsa, gwamnatin jihar ta ɗauki matakan daƙile ƙaruwar ambaliyar, da suka haɗa da gyaran magudanan ruwa da kuma wayar da kan jama’a kan lamarin.
Ya kuma yi kira ga mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su gaggauta yin ƙaura.
“Na zo ne a yau don magance mummunar ambaliyar da ta shafi ƙananan hukumomin Sabon-Gari da Zariya a ranar Litinin.
“Duk da ƙoƙarin da muka yi na ganin an shawo kan lamarin, ambaliyar ta yi ɓarna sosai, inda sama da gidaje 200 suka lalace.
“Kamar yadda za ku iya tunawa, mun samu hasashe daga Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) watanni uku da suka gabata, kuma mun ɗauki matakan da suka dace don tunkarar ambaliya,” in ji shi.
Daga nan sai ya buƙaci mazauna yankin musamman manoma da su yi amfani da sauran filayen da gwamnatin jihar ta ba su domin noma tare da komawa cikin birane.