Shugabannin yankin Arewa ta tsakiya sun sanar da ficewarsu daga Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) a kokarinsu na hada sabuwar kungiya.
Sabuwar tafiyar na daya daga cikin irin matakan da yankin ke kokarin dauka domin shawo kan matsalar tsaron da ta ke neman addabarsu.
Aminiya ta gano cewa sabuwar kungiyar za ta kasance ba ta da wata alaka da siyasa kuma za a kafata ce domin hada kan kabilun da ke zaune a yankin da nufin ganin an dawo da zaman lafiya.
Tuni dai aka bayyana Jerimiah Useni a matsayin shugaban kwamitin amintattun kungiyar, yayin da tsohon karamin ministan lafiya Gabriel Aduku kuma zai kasance sakataren riko.
Da yake yi wa ’yan jarida jawabi a Abuja ranar Laraba, Jerimiah Useni ya ce, “A kan haka ne muka ga ya wajaba mu tashi tsaye wajen kafa kungiyarmu da za mu rika jawo hankalin hukumomi su magance tarin matsalolin da ke ci mana tuwo a kwarya.
“Saboda haka babu wata gudunmuwa da za a ce ta yi kadan daga bangarenmu wajen ba mutanenmu irin kariyar da suke bukata daga garemu a matsayin shugabanni.
“Za mu taimaka tare da ba Gwamnatin Tarayya cikakken hadin kai wajen samar da ayyukan raya kasa da kuma damawa da mutanenmu a kan abubuwan da suka shafi kasa”, inji shi.
Shi kuwa a nasa bangaren, Gabriel cewa ya yi yankin na da muhimman albarkatu da ya kamata su mayar da shi cibiyar siyasa, tattalin arziki da zamantakewar Najeriya.
Sai dai ya ce abin takaici ne yadda kalubalen tsaro ke ci gaba da barazana ga cigaban yankin ta kowace fuska.
Ya ce, “Ta bangaren tsaro, a bayyane yake cewa kusan dukkannin jihohin yankin na fama da matsalar kashe-kashe da ta garkuwa da mutane akai-akai. Rayukan jama’ar yankinmu yanzu ba su da wata daraja.
“Daga yanzu, shugabnnin wannan sabuwar kungiyar sun gaji da gafara sa ba su ga kaho ba. Dole a kawo karshen wadannan kashe-kashen”, nji Gabriel.