Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta fara aikin cire sunayen wadanda ba su kai shekarun kada kuri’a ba daga kundinta.
Kwamishinan INEC kan Yada Labarai da Ilimantar da Masu Kada Kuri’a, Festus Okoye ne ya bayyana haka yayin tattaunawar da aka yi da shi a Tashar Channels TV.
- Yadda aka hallaka ’yan Boko Haram da sabbin sansanoninsu a Borno
- CBN ya haramta cirar sabbin kudi a cikin banki
Da yake amsa tambaya, Okiye ya ce, “Dangane da batun kada kuri’ar wadanda shekarunsu ba su kai ba, hukumar ta wallafa duk sunayen da ta yi wa rijistar zabe a cibiyoyinta a kananan hukumomi.
“Jama’a sun kawo korafe-korafensu, yanzu haka hukumar na kokarin tsaftace rijistarta. Za mu yi bakin kokarinmu wajen tabbatar da amfani da rijistar da ’yan Najeriya za su yi alfahari da ita.”
Game da batun kada kuri’ar baki daga ketare, jami’in ya ce “Wadanda ke da sahihin katin zabe kadai za su kada kuri’a a zaben 2023.
“Don haka ’yan Najeriya su sanya ido, duk wani bako da suka gani a wajen kada kuri’a su sanar da jami’an tsaro.”