Manajan Daraktan Kamfanin Sufurin Jiragen kasa na Najeriya (NRC), Injiniya Fidel Okhiria, ya ce sun dade suna hulda da mahukuntan Tashar Teku-Huta ta Kaduna.
Mista Okhiria, wanda ya bayyana cewa dangantakar ta kullu ne tun ma kafin a gina tashar, inda ya ce kamfanin yana aiki wajen bunkasa ayyukan sauke sundukai a tashar kafin a sake yi mata sabon fasali.
Ya yi alkawarin cewa za a samu ingantuwar hulda daga bangaren Kamfanin NRC, sai dai ya ce ba nan take komai zai kankama ba, amma ya bayar da tabbacin cewa irin goyon baya da tallafin da mahukuntan Kamfanin NRC ke samu daga gwamnati, za a samu nasarar hakan.
“Za mu sadaukar da kanmu, mu yi kokarin ganin ba mu bai wa ’yan Najeriya kunya ba. Zan iya cewa cikin sa’o’i 36, za mu iya kai sundukan kaya tashar Teku-Hutar. Na iso nan ne tare da Daraktan Aiwatar da Ayyuka ta yadda zai ji ra’ayoyin wadansu, kuma ya lura da yadda za mu kara bunkasa dimbin damar da za a iya samu a tashoshin Teku-Hutar.
“Abin da zai ba ku sha’awa da ya kamata ku sani a bana, za mu kawo taragun 20 na sundukai 20, wadanda za su fi wadanda muke da su a halin yanzu. Sannan muna kokarin dawo da jirgin kasan da ya tsaya a Maiduguri. Al’amarin ya auku ne mako biyu kafin matsalar rashin tsaro ta auku. Muna matukar kokarin dawo da shi ta yadda za mu sanya shi a jerin jiragenmu,” inji shi.