Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cire ’yan Najeriya miliyan 10.5 daga kangin talauci cikin shekara biyu.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabansa na Ranar Dimokuradiyya.
- Ranar Asabar ce 1 ga watan Dhul Qadah 1442 —Sarkin Musulmi
- Ganduje ya sha alwashin hukunta masu daukar nauyin fadan daba a Kano
“Zan fara kasancewa mutum na farko da zai sanar da ci gaban da aka samu duk da karancin abubuwa da muke da su.
“Burinmu shi ne cire mutum miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekara 10 duk da kalubalen cutar COVID-19.
“A cikin shekara biyu mun cire mutum miliyan 10.5 daga talauci da suka hada da manoma, masu kananan sana’o’i, ‘yan kasuwa, mata da sauransu.
“Ina da yakinin za mu cimma burin cire mutum miliyan 100 daga kangin talauci karkashin tsarin cire mutane daga talauci na gwamnatin tarayya kuma nan gaba za mu bayyana matakan da muka bi wajen cimma wannan nasara.
“A shekarar da ta gabata ne Najeriya da ma kasashen duniya sun fuskanci koma bayan tattalin arziki sakamakon annobar cutar COVID-19 wadda ta zo mana a bazata ba tare an shirya mata ba,” a cewar Shugaba Buhari.