Babban Bankin Najeriya (CBN), ya musanta zargin da wasu ’yan Najeriya ke yi na cewar ana fama da karancin sabbin takardun kudi.
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, wanda Musa Jimoh, Daraktan Sashen Kula da Tsarin Biyan Kudi na bankin ya wakilta, ya musanta zargin a wani taron manema labarai a Jos.
- Kwallon Kashu zai kawo wa Najeriya $500m bana —Ministan Noma
- NAJERIYA A YAU: Yadda INEC za ta kare ma’aikatanta daga barazanar tsaro lokacin zabe
“CBN ta bai wa bankunan kasuwanci sabbin takardun kudi domin sakawa a na’urar cire kudi ta ATM.
“Wannan shi ne zai sa kudin su yi saurin zagaya wa a tsakanin al’umma kuma muna gargadin bankuna da su daina boye sabbin kudanen ko kuma su fuskanci hukunci,” in ji shi.
Emefiele ya shawarci ‘yan kasar nan da su yi gaggawar mika tsofaffin kudadensu ga bakuna don karbar sabbi kafin cikar wa’adin daina amfani da su a ranar 31 ga watan Janairu 2023.
Gwamnan CBN ya bayyana cewa matakin na sauya fasalin kudin ya yi daidai da tsarin duniya, inda ya kara da cewa ya kamata ake sauya fasalin kudi duk bayan shekara biyar.
Sai dai ya ce an kwashe shekara tara a Najeriya ba tare sa sauya fasalin kudade ba
Da yake jawabi yayin wani rangadin sanya ido da wayar da kan jama’a da aka gudanar a wasu wurare a garin Jos, gwamnan CBN, ya bayyana cewa matakin sauya fasalin manyan kudin kasar nan wani aiki ne na kasa baki daya da nufin magance matsalolin da suka shafi yaduwar kudade.
Ya ce matakin zai magance kalubalen tsawaita ajiyar kudi a bankuna, tara kudi da kuma abubuwan da suka shafi buga jabun kudi.