Ofishin Kula da Basuka na Jihar Kano, ya sanar da cewa ya biya sama da Naira biliyan 63 na basukan cikin gida da na waje da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta karɓo.
Babban daraktan ofishin, Dokta Hamisu Sadi Ali ne, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai.
- Masu hakar ma’adinai 13 sun rasu bayan ruftawar kasa a Filato
- Lakurawa na da jirgi mara matuki, sun karɓe iko a kauyukan Kebbi —Bukarti
Ya yi bayanin cewa, duk da cewa gwamnatin yanzu ta gaji bashi mai tarin yawa, amma ta rage bashin sosai.
Haka kuma, ya jaddada cewa gwamnati mai ci ba ta karɓo wani sabon bashi tun lokacin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya hau mulki ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Ya ce, “Tun bayan da gwamnatin NNPP ta hau mulki, ba a sanya hannu kan wani sabon bashi ko karɓo wani bashi daga ciki ko wajen ƙasar nan ba.”
Dokta Ali, ya bayyana cewa gwamnan ya biya bashin ƙasashen waje sama da Naira biliyan 3.5.
Har ila yau, ya ce gwamnatin ta biya bashin cikin gida na sama da Naira biliyan 60 a farkon rabin shekarar 2024, wanda hakan ya rage jimillar bashin zuwa kimanin Naira biliyan 127.8.
Haka kuma ya jaddada cewa Dokar Kula da Basukan Jihar Kano ta 2021, ta bai wa Ofishin Kula da Basuka ikon karɓo bashi a madadin jihar, idan buƙatar hakan ta taso.
Dokta Ali, ya bayyana cewa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, ta sanya hannu kan yarjejeniyar bashi a 2018 tare da Hukumar Ci Gaban Faransa don karɓo bashin kusan Yuro miliyan 64 don aikin ruwa.
Ya jero bashin ƙetare da ake bin Kano a yanzu, wanda aka karɓo domin yin hanyoyi, shirin yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro, ilimi, noma, daƙile zaizayar ƙasa, da kula da ruwa, wanda aka karɓar wa hukumomi daban-daban bashin.
Ya bayyana cewa babu wata gwamnati a tarihin Kano da ta taɓa karɓo bashi daga bankunan cikin gida sai gwamnatin Ganduje.
Ya ce gwamnatin ta baya ta karɓo basuka shida daga bankuna daban-daban, ciki har da Access Bank da Fidelity Bank don ayyukan gine-gine, albashi, da kasafin kuɗi.