Akalla mutum uku ne suka jikkata a wani mummunan rikici da ya kaure tsakanin makiyaya da manoma mazauna Iddo, wata alkarya da ke Babban Birnin Tarayya na Abuja a ranar Litinin.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, ASP Mariam Yusuf ce ta ba da tabbacin hakan da cewa kura ta lafa a yayin da Kwamishinan ’Yan Sanda Ali Chiroma tuni ya jagoranci wani zaman sulhu tare da Shugabannin yankin na Iddo domin guje wa faruwar hakan a gaba.
Bukkoki da dama aka kona a yayin da mazauna yankin suka gwabza da Fulani makiyaya da ake zargi suna kada dabbobi kiwo a gonakinsu.
Sanarwar da ASP Mariam ta fitar ta ce, “Rundunar ’yan sandan Abuja ta samu nasarar kwantar da tarzomar da ta kunnu a garin Iddo biyo bayan rikicin makiyaya da manoma da ya barke tsakanin mazauna yankin a ranar Litinin.”
“Wannan mummunan lamari ya bar mutum uku cikin raunuka daban-daban baya ga wasu bukkoki da aka kona a yankin.”
“Kwamishinan ’Yan Sanda Bala Chiroma ya ba da umarnin gudanar da binciken diddigi a kan lamarin,” inji ASP Mariam.