Alhaji Isah Muhammad Ashiru tsohon dan Majalisar Jihar Kaduna ne, kuma ya taba zama dan Majalisar Wakilai, kafin ya yi takarar neman zama Gwamna Jihar Kaduna a zaben shekarar 2019 a Jam’iyar PDP. A zantawarsa da Aminiya ya zargi gwamnatin APC a jihar kan yadda take tafiyar da mulkinta inda ya ce mulkin soja ake yi a jihar ba dimokuradiyya ba:
Me kake ciki tun bayan faduwarka zaben 2019?
Bayan zaben 2019 na yi tunanin komawa gona da harkar kasuwanci na saye da sayarwa. Tun zuwan wannan gwamnati, sai na ga lokaci ne da zan zauna da iyalaina in huta na wani lokaci.
Amma daga wancan lokaci zuwa yanzu jam’iyarmu ta yi nasarar gudanar da zaben
shugabanninta da za su tafiyar da harkokinta.
Me ya sa kake ji ya jawo ka fadi a shekarar 2015 da 2019 da ka fito takarar Gwamna?
A shekarar 2015 tun a zaben share-fage na fadi, inda Malam Nasir El-Rufa’i ya yi nasara a APC, na kuma ci gaba da zama a jam’iyyar har kafuwar gwamnati. Amma suna ganin ba mu da amfani, saboda haka ba ni da wani zabi, sai na bar jam’iyyar, na dawo Jam’iyyar PDP da kowa ya san ni a cikinta, jiga-jigan jam’iyyar ne suka nemi in dawo gida.
A Lokacin zaben share-fage a PDP na samu nasara a cikin mutum tara, kuma kuri’ar da na samu ta ba ni mamaki matuka sannan abokan takarata nan take suka karbe ni, na kuma yi musu alkawari yin aiki tare da su. Ni na san mun ci zabe a shekarar 2019, amma duk abin da ya faru ya zamo tarihi yanzu, kuma ban yi da-na-sani ba.
Akwai maganar da ake yi cewa an ki zabenka ne saboda kana da saukin kai. Ina gaskiyar zancen?
Ba sai na kasance marar mutunci ba, kafin in nuna wa mutane ina da zafi. Kuma ina amfanin yin zafi ga jama’ar da za ka shugabanta? Me ya sa zan zama mai zafi bayan gwamnati ta mutane ce? A matsayin Gwamna, ba ni kadai zan mulki jihar ba.
Matsalar da muke fama da ita, shi wannan Gwamna ba ya neman shawarar kowa a jihar. Shi ba mutum ne mai sauraren mutane ba.
Yanzu mulkin da ake yi a Jihar Kaduna, ya yi kama da mulkin soja, abin da ake so kawai shi ne ka yi biyayya ba tare da yin tambaya ba. Wannan ba mulkin
dimokuradiyya ba ne.
Ba sa son a fadi laifinsu, kuma ba sa sauraren mutane saboda suna tunanin sun fi kowa sani. Tsare-tsaren da APC take gudanarwa a matakin jiha da tarayya abubuwa ne da ba sa yi wa mutane dadi.
Allah ne kawai zai ceci kasar nan daga matsalolin da ake ciki a yanzu, matsalar ita ce a matakin tarayya babu wanda za ka nuna a matsayin jagora. A Jihar Kaduna ma abin da sauki tunda ana ganin El-Rufa’i a ko’ina da za a iya nunawa.
Ke nan kana zargin jam’iyya mai mulki a kan duk abin da yake faruwa a kasar nan?
Sun samu mulkin ne a lokacin da ba su yi tsammani ba, kuma ba su san za su iya cin zabe ba, shi ya sa ba su shirya wa aikin ba. Sun samu mulkin amma sun rasa
yadda za su tafiyar da shi.
Duk ayyukan da suke akwai son rai na wadansu mutane kadan daga cikinsu, don amfanin kansu kurum. PDP ta mika mulki lokacin man fetur yana Naira 67, amma a yau farashin da suke tunanin mayarwa shi ne Naira 385 a kan kowace lita, ci gaba muke yi a haka? Ana sai da Dala lokacin da aka mika musu mulki a kan Naira 215, kwana biyu da suka wuce, Dala ta kai Naira 503.
A Kaduna sun yi alkawarin daukar ma’aikata da rage talauci, wane yanayi ake ciki yau a Jihar Kaduna? Ku dubi yadda wani kawai yana zaune a ofishinsa, a matsayin shugaban ma’ aikata, amma ya kori malaman jami’a don sun shiga yajin aiki. Yaya za ku kwatanta wannan yanayi da lokacin mulkin PDP.
Jami’ar Jihar Kaduna, PDP ce ta gina ta, saboda bai wa ’ya’yanmu damar yin karatu da kudi kalilan. Amma a yanzu fa? An samar da ayyukan yi ga mutanenmu da yin nazari don ci gaba. Me APC suke yi a yanzu idan aka kwatanta da abin da muka yi? Ina ba wa Gwamna shawara ya dubi baya, zuwa yanzu don samun zaman lafiya.
Na ga wasikar da Shugaban Kungiyar Kwadago ya rubuta wa Shugaban Kasa, a kan saba alkawari da gwamnatin jihar take yi, bayan tattaunawa da suka yi da kungiyar.
Sun ce yajin aiki na sharar-fage, domin muddin gwamnatin ba ta cika sharuddan da aka yi ba, za su tafi yajin aiki a matakin kasa.
Gaskiya ni ba na goyon bayan yajin aiki a matakin kasa baki daya domin zai iya karya gwamnati. A halin yanzu mutane suna cikin talauci da rashin tsaro, shekara daya da rabi ke nan rabon da in je gonata.
Masu garkuwa da mutane suna nan suna kama jama’a, idan sun dauki mutum sai dai ka ji ana maganar Naira miliyan 50.
Ni in sun dauke ni kudin sai ya fi haka. Ba a samun abubuwa da sauki a kasar nan, amma na Kaduna ya fi muni, don ba gidan da wannan yanayin bai shafa ba, na tsarin APC, satar mutane, kashe-kashe da rashin ruwan sha, babu kiwon lafiya da suka yi alkawari, batun samar da ilimi kyauta, babu shi, sai dai ma karin kudin makaranta da aka yi.
Masarautun gargajiya aka fara tabawa, sai ma’aikatan gwamnati, yanzu kuma suna fada a kan dalibai. Ba mu san da wa za su yi a nan gaba ba. Ba a maganar masu gidaje da filayen wadanda aka kwace musu nasu.
Yaya kake tunanin za a iya magance matsalolin, in ka yi la’akari da rashin kudin shiga a jihar?
Za mu fara ne da ga farko, domin ya taba muhimman wurare da suke samar da kudin shiga ga jihar. Mutane na barin Kaduna, musamman masu kananan masana’antu, wadanda suke samar da kudin shiga ga
gwamnati. ’Yan kasuwan da suke Titin Waff ina suke a yanzu? Je ka Babbar Kasuwar Kaduna da take a cikin gari ka ga abin da yake faruwa. Ya karbe duk wasu wurare ya bai wa mutane da ba ’yan jihar ba ne.
Kaduna ta rasa kashi 70 na kananan ’yan kasuwarta, yanayin da ya sa da yawansu suka koma Kano da Katsina da wasu wurare da suke tunanin za su samu yanayin yin kasuwan ci mai kyau.
Ban yarda kudin shiga ya ragu ba, su suka takura wa mutane suka fice daga jihar amma duk wannan za mu daidaita shi idan aka sake ba mu dama.
Mene ne ra’ayinka game da biyan kudin fansa da kuma yin sulhu da masu garkuwa da mutane?
Abin mamaki, mutumin da ya ce kada mu yi sulhu shi ne wanda ya fara tattaunawa a lokacin rikicin Kudancin Kaduna, ya fito a gidan talabijin bayan ya san ba ya da iko da jami’an tsaro.
Wasu maganganun ba su dace a yi su a waje ba, musamman harkokin da suka shafi tsaro, amma ya fito ya ce shi zai fuskance su wuta-da-wuta, yanzu wa yake cutuwa? Duk Gwamnan da ba zai iya kare
rayuka da dukiyar mutane ba, ba ya da hurumin zama a kujerar mulki.
A ganina yin sulhu daya ne daga cikin hanyoyin magance matsalar. Mutane na cewa PDP ta yi shiru a Jihar Kaduna, kana ganin jam’iyyar na da karfin sake karbar mulki a 2023?
A siyasa mun yarda da tsari da dabaru, wadansu na amfani da ta’adanci a kan abokan hamayya, ba na tunanin irin haka
ci gaba ne. Ban ga dalilin da zai sa in zagi Gwamna El-Rufa’i da gwamnatinsa ba, don ina wata jam’iyya. Wane canji yin hakan
zai kawo? Shi ba zai ma saurare ka ba.
Idan ka lalata shirye-shiryensu amfanin me zai maka ko zai yi wa al’umma? Na tuna wani abin da ya faru, lokacin da muka je Cibiyar ’Yan jarida (NUJ) ta nan Kaduna, suka turo aka tarwatsa mu. Mu ba za mu yi musu haka ba.
A ganina ilimantar da mutane da nuna musu yadda gwamnati take tafiya zai fi muhimmanci. Gwamna El-Rufa’i ya jagoranci zanga-zanga da yawa a Kaduna,
lokacin da PDP take mulki, amma yanzu yana zargin PDP da shirya masa yajin aikin gargadi na kwana uku da ’yan iwadago
suka yi.
Me ya sa kake son zama Gwamnan Jihar Kaduna?
Ina cikin gwamnati da dadewa, kuma na san gudunmawar da na bai wa gwamnatocin baya har suka samu nasarori, wanda hakan ne ya sa nake ganin idan aka ba ni dama zan yi abin da ya fi nasu saboda kwarewata.