Biyo bayan sanarwar Gwamnatin Jihar Kano ta sanya ranar Lahadi a matsayin ranar da za a gudanar da mukabala tsakanin Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara da sauran malaman jihar Kano, malamin ya ce ya amsa gayyatar kuma a shirye yake ya halatta bisa wasu sharudda.
A ranar Lahadin data gabata ne dai Kwamishinan Harkokin Addini na Jihar, Dakta Muhammad Tahar Adam ya damkawa malamin takardar gayyatar, abin da ya jima yana kira da a shirya.
- Ganduje ya sanya ranar mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da Malaman Kano
- Yajin aiki: Kayan abinci sun yi tashin gwauron zabo a Kudu
A kwafin amsar wasikar da ya aikewa da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, Sheik Abduljabbar ya ce, “Na rubuto domin in nuna godiyata da matakin da mai girma Gwamna ya dauka da kuma damar da aka ba ni, saboda hakan ne zai kawo fahimta da kuma masalaha a lamarin, musamman la’akari da cewa an ba dukkan bangarorin da lamarin ya shafa dama iri daya.
“Ina amfani da wannan damar wajen sanar da mai girma Gwamna cewa ina daukar batun Ma’aiki (S.A.W) da na Sahabbansa da matukar muhimmanci kuma ban taba yin wani abu da zai taba darajarsu ba.
“A kan haka, na amsa wannan gayyatar kuma zan halarci mukabalar da zuciya daya, ina fatan sauran wadanda za mu fafata da su suma za su zo da zuciya daya.”
Sharuddan da Sheik Abduljabbar ya gindaya
“Yayin da nake godewa mai girma Gwamna saboda ba ni damar zuwa da littattafaina domin bayyana sahihanci, madogara, nagarta da kuma gaskiyar hujjojina, ina kuma rokon da a kyale ni na zo da mutanen da za su kular min da wadannan littattafan, su kuma dauki sautin murya da na bidiyo yayin mukabalar,” inji shi.
Aminiya ta gano cewa mukabalar dai zata gudana ne a ranar Lahadi, bakwai ga watan Maris na 2021 a Fadar Sarkin Kano da misalin karfe 9:00 na safe kuma za a watsata kai tsaye ta kafafen watsa labarai na gida da na ketare.
Kazalika, Babban Limamin Kano, Farfesa Muhammad Sani Zahraddeen da Babban Mai ba da Fatawa na Babban Masallacin Kasa dake Abuja, Farfesa Shehu Galadanci ne za su gudanar da alkalanci yayin mukabalar.
A cikin watan da ya gabata ne dai Gwamnatin Kano ta sanar da dakatar da malamin daga gudanar da wa’azi a jihar saboda zargin da ta yi cewa zai iya tayar da zaune tsaye.