✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mujallar Faransa ta fitar da sunayen ’yan kwallon da za su fafata a Gasar Gwarzon dan kwallon Duniya

A ranar Litinin da ta wuce ne Mujallar da ake wallafawa a Faransa ta fitar da jerin sunayen ’yan kwallo biyar da za su fafata…

A ranar Litinin da ta wuce ne Mujallar da ake wallafawa a Faransa ta fitar da jerin sunayen ’yan kwallo biyar da za su fafata a Gasar Gwarzon dan kwallon Duniya na bana. A duk shekara Mujallar ce take daukar nauyin gudanar da gasar zabo Zakaran dan kwallon duniya da ake yi wa lakabi da Ballon d’Or. A ’yan shekarun baya, Mujallar ta yi hadin gwiwa da Hukumar kwallon kafa ta Duniya inda ake kiran gasar da FIFA Ballon d’Or amma a bara ne suka yi hannun riga inda kowane bangare yake gudanar da gasar a matsayi na kashin kansa.

’Yan kwallon da mujallar ta fitar  da sunayensu su ne Lionel Messi dan asalin Ajantina da ke buga wa FC Barcelona na Sifen kwallo, sai Cristiano Ronaldo, dan asalin Fotugal da yake yi wa kulob din Real Madrid na Sifen kwallo sai Neymar, dan asalin Brazil da ke buga wa kulob din PSG na Faransa kwallo.

Sauran su ne Paulo Dybala dan asalin Ajantina da ke wasa a kulob din Jubentus na Italiya da kuma N’Golo Kante, dan asalin Faransa da ke wasa a kulob din Chelsea na Ingila.

Ga dukkan alamu Cristiano Ronaldo ne zai sake lashe wannan gasa a karo na biyar bayan ya taimaka wa kulob din Real Madrid na Sifen wajen lashe Kofin Zakarun Kulob na Turai (Champions League) a bara da kofin Gasar La-Liga ta Sifen da kuma wadansu kofuna.

Idan Ronaldo ya samu nasara, zai yi daidai da Messi a wajen yawan lashe gasar sau biyar-biyar kenan.