✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimmancin hadin da ake yi wa fuska da yadda ake hada su

Hadin da ake yi wa fuska na nan da dama. Ya kamata zuwa yanzu masu karatu su gane wane irin hadin nake nufi. Amma idan…

Hadin da ake yi wa fuska na nan da dama. Ya kamata zuwa yanzu masu karatu su gane wane irin hadin nake nufi. Amma idan akwai wadanda ba su san wannan hadi ba, zan yi musu bayani.  A takaice dai hadin fuska, shi ne, irin-kwabe-kwaben da ake yi a shafa a fuska domin magance wasu cututtukar da ke damun fatar jiki ko ta fuska.
Wannan hadin na cire kwayoyin cutar da ke cikin fata da gyara shi da kuma kara karfafa karfin fata. Ba tare da an kashe kudi a kantuna sayen maganin gyaran fata ba, akwai yadda za a iya hada wannan hadi ta hanyar amfani da kayan girki kamar haka:
•    Za a iya hadin ruwan lemun tsami da na zuma sannan a shafa a fuska ko jiki, domin inganta hasken fata da karfafa fatar jiki da kuma hana fesowar kuraje.
•     Akwai hadin ayaba da kwaiduwar cikin kwai da  man zaitun. Idan aka yi wannan hadin, sai a shafa a fuska na tsawon minti ashirin sannan a wanke, shi ma wannan hadin domin gyaran fatar jiki da kuma na fuska ne.
•    Hadin ruwan lemun zaki da ruwan kwai da kuma kurkum na da matukar muhimmanci sosai domin yana taimakawa wajen gyaran fata, musamman ma ga amare.
•    Garin bawon lemu wanda sai an busar sannan a daka a tankade sannan a hada da ‘baking soda’ shi ma yana magance cututtukan fata sosai.
•    Akwai hadin ruwan kwakwa da garin bawon lemun zaki da kuma madara. Wannan irin hadin na sanya fata sulbi sosai.
•     Hadin fiya da man zaitun da madara na da muhimmanci sosai ga inganta fata domin na magance gautsin fata da kuma sanya fata taushi.
•     Ayaba da ruwan lemun zaki da kuma kindirmo idan aka kwaba su ana shafawa a jiki na magance tattarewar fata.