Masu ruwa da tsaki a harkar sanin darajar alkama sun bayyana cewa, aiki tukuru tare na da matukar muhimmanci wajen samun nasarar noman alkama da wadatuwarta a Najeriya.
Wannan kiran ya fito ne daga masana da suka ba da fifikon samar da wadatuwar alkama a kasar a karo biyu kan taron karawa juna sani na Olam Green Land Webinar Series.
Taron mai taken: “Sake Tunanin Noman Alkama a Najeriya – Samar da iri, Tsari na Bincike, Hadin gwiwa da Abokan Hulda”, an gudanar da shi ne a ranar Laraba, 24 ga Nuwamba, 2021.
Masanin noman alkama samfurin durum kuma tsohon Shugaban hadin gwiwar Italiya a Habasha, mai suna Tiberio Chiari wanda shi ne babban mai gabatarwa a taron da aka yi a yanar gizon, ya ce kula da inganci, iri masu dacewa da ake bukata, tsarin kulawa mai kyau, hadin gwiwar kananan manoma zuwa ga manyan manoma, ingantattun wuraren adana hatsin.
Samuwar kudaden saka hannun jari, tsare gaskiyar manoma da sauransu, su ne manyan ginshikan samun nasara yayin da ake yin yunkurin aiwatar da tsarin kasuwancin iri na al’umma da za a wadata.
Ya bayyana alfanun da ke tattare da yin aiki tare da manoma masu karamin karfi wajen bunkasa harkar darajar alkama.
Da yake ambaton kasar Habasha a matsayin nazari, Chiari ya ce, “Akwai tattalin arziki mai girman gaske wajen mu’amala da kungiyoyin hadin gwiwar manoma maimakon yin aiki da manoma daidaiku, kuma masu ruwa da tsaki na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da gudanar da aikin yadda ya kamata don samun sakamako mai kyau.”
Wani babban masanin kimiyya a Cibiyar Nazarin Aikin Gona ta Senegal (ISRA), Dokta Sall Amadou Tidiane, ya yi bayani game da yadda harkar darajar alkama a Senegal ta inganta.
Ya ce, ta hanyar bin tsarin sana’ar yaduwar irin alkamar a kasar ta bunkasa daga noman alkama a shekarar 2017 zuwa ga manoma 2,000 sun yi noman alkamar cikin nasara a shekarar 2021.
Ya bayyana cewa, yin amfani da kwazon mata masu karamin karfi na gida zai haddasa yaduwar tasirin sababbin iri don samun yawan noman su.
Babban masanin kimiyya a Cibiyar Bincike kan aikin gona ta Kasa da Kasa a wuraren busassun International Centre for Agricultural Research in Dry Areas (ICARDA), Dokta Filippo Bassi, babban abokin hadin gwiwa wajen samar da iri masu dacewa da irin yabanyar da ake bukata a shirin samar da alkama, ya ce burin Olam shi ne samar da fiye da tan dubu 200, na alkama da darajarsu ta kai Dala miliyan 70, yayin da ya himmatu wajen ba da horo ta shirin horar da manoma dubu 50 kafin shekarar 2030.
Manajan Darakta na Kamfanin Crown Flour Mill Limited (CFM), Mista Ashish Pandem, ya ce “An dauki hanyar dinke babban gibin da aka samu wajen noman alkama a kasar nan.
Wannan hadin gwiwar masu ruwa da tsaki wani mataki ne da ke kan hanya madaidaiciya.
Zurfafan jarin da muke bayarwa wajen samar da iri masu dacewa da yanayin Najeriya da kuma yin amfani da sana’ar samar da iri na al’umma zai bayyana a cikin ci gaban noman alkama nan da shekaru masu zuwa.”
Manajan Daraktan Kamfanin CFM ya ci gaba da cewa, jarin da Olam ya bayar na Naira miliyan 300 wajen binciken iri da kuma bullo da wani sabon sana’ar iri ta al’umma da za ta yi amfani da kwazon kungiyoyin mata masu kananan sana’o’i na manoma yana da tasiri mai karfi kan rayuwar al’ummar manoma da kuma burin da za a cimma ga Gwamnatin Tarayya ta fuskar samar da ayyukan yi da samun wadatar abinci da tanadar wadatuwar abinci cikin shekaru sama da goma.
Dokta Kachalla Kyari Mala, shi ne jagoran bincike na shirin aikin wadatar alkama kuma Babban Jami’in Bincike na Cibiyar Nazarin Tafkin Chadi (LCRI), ya bayyana karancin fahimtar manoma da mafi kyawun ayyukan noma a matsayin daya daga cikin abubuwan da ke haifar da karancin amfaninsu.
Ya ce, “Sanya manoma a tsarin da ya dace lokacin da ake bukata da fara daukar manyan hanyoyin bunkasa iri har zuwa lokacin girbi zai taimaka musu wajen fahimtar da mafi kyawun tsarin kulawa da aikin gona.