✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimman labarun mako cikin hotuna

Muhimman abubuwan da suka faro a mako, cikin hutuna.

Wasu muhimman abubuwa da suka faru a makon da muke ciki dun dauki hankali matuka.

Ga hotunan wasu daga cikinsu da Aminiya ta tattaro:

‘Yan bindiga sun fito da sabon bidiyon daliban da suka sace daga Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Afaka, Jihar Kaduna.
Najeriya ta bukaci taimakon sojin Amurka a yaki da ta’addanci tare da neman rundunar AFRICOM ta dawo da zama a Afirka. Shugaba Buhari ne ya bayyana haka yayin ganawarsa da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken.
An bindige Auwalu Daudawa, mutumin da ya kitsa tare da jagorantar sace Daliban Kankara, kasa da kwana biyar da komawarsa daji bayan ya yi tubar muzuru.
Dubun dubatar mutane sun halarci jana’izar Mai Babban Daki, mahaifiyar Sarkin Kano, Hajiya Maryam Ado Bayero.
Kungiyar Dattawan Jihar Borno sun zargi jami’an gwamnati da yi wa jami’an tsaro zagon kasa a yaki da Boko Haram.
Gwamnatin Jihar Katsina ta haramta yin tashe a watan Ramadan din bana saboda dalilan tsaro.
An sa zare tsakanin Fadar Shugaba da Rabaran Ejike Mbaka, wanda ya yi fice wurin ganin an zabi Buhari a 2015. Mbaka ya nemi Buhari ya sauka daga mulki saboda a cewarsa, Allah Na fushi da Shugaban Kasar. Amma Fadar Shugaban Kasa ta zarge shi da yin kalaman ne bayan ya nemi kwangila gwamnati ta hana shi, har ta yi barazanar kai kararsa ga Fadar Fafaroma.
‘Yan bindiga sun sake kashe mutum biyu daga cikin daliban Jami’ar Greenfield da suka sace a Jihar Kaduna, ‘yan kwanaki bayan sun kashe uku daga cikin daliban. (Hoto: Nasu Bir/AFP)
Hukumar Zabe ta Kasa, INEC, ta sanar cewa za ta gudanar da Babban Zabe mai zuwa a shekarar 2023.
An dage ci gaba da taron Majalisar Tsaro ta kasa zuwa ranar Talata na mako mai kamawa.
Dubban mazauan Geidam sun tsere bayan kungiyar Boko Haram ta mamaye garin, inda mayakan kungiyar suka raba wa mutane kudade, tare da hallaka malamai.