A wannan shekara da muke bankwana da ita ta 2022 ce manyan jam’iyyun Najeriya na APC mai mulki da PDP ta adawa suka gudanar da babban taronsu na kasa, wanda ya samar Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar a matsayin ’yan takarar shugaban kasa a zaben 2023.
PDP ta fara gudanar da taronta a ranar 28 ga watan Mayun wannan shekara da muke bankwana da ita, inda Atiku Abubakar, Aminu Waziri Tambuwal, Bukola Saraki da kuma Nyesom Wike suka fafata.
- An yanke wa ’yan kungiyar IS 17 hukuncin kisa a Libya
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kan Ranar Kyauta A Addinin Kirista
Sai dai Atiku ya doke Gwamnan Ribas, Wike da kuri’a 371 daga cikin kuri’a 767 da wakilan PDP suka kada, inda Wike ya karkare da kuri’a 237.
An shiga takun saka tsakanin Wike da Atiku
Wike ya shiga takun saka da Atiku ne tun bayan kammala zaben fid-da-gwanin jam’iyyar PDP da ya gudana a watan Mayu, inda ya sha kaye a hannun Atikun.
Takun saka tsakaninsu ya yi tsami tun bayan da tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya zabi Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin abokin takararsa, a maimakon shi Wiken.
Tun daga lokacin, Gwamnan na Ribas ya ja layi da Atiku da kuma Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu.
Wike da wasu Gwamnonin PDP hudu da ake wa lakabi da G-5 sun lashi takobin ganin bayan shugabancin Ayu.
A watan da ya gabata, Wike ya yi alkawarin mara wa ’yan takarar shugaban kasa na jam’iyyun LP da NNPP, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso baya a zaben 2023.
APC ta shiga lalube
Duk da cewa kwana bakwai ya rage APC ta yi nata zaben fid-da dan takarar Shugaban Kasa a wancan lokaci, amma Aminiya ta gano cewar babu wani kwakkwaran motsi da jam’iyyar ta fara game da taron.
Jagorori da masu neman takara da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar sun samu rabuwar kai game da abin da za su yi.
Uwa uba, an dage ranar da aka sanya na tantance mutum 23 da ke neman takarar Shugaban Kasar da aka shirya gudanarwa ranar Litinin din bayan zaben PDP, har sai abin da hali ya yi.
Ga shi kuma Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar (NWC) wanda tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, bai nada kwamitin da zai yi aikin ba, ballantana sanya sabuwar ranar da za a yi tantancewar ba.
Daga cikin mutum 23 da ke neman tikitin takarar a jam’iyyar, masu ruwa da tsaki sun fi karkata kan Jagoran jami’iyyar na Kasa, Bola Ahmed Tinubu; Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo; Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan da kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.
Tinubu ya zama dan takarar APC
A ranar 8 ga watan Yuni ne Tinubu ya lashe zaben fid-da-gwanin da jam’iyyar APC ta gudanar, inda ya doke masu neman kujerar takarar Shugaban Kasa 13 na jam’iyyar a zaben da ya gudana a Abuja.
Tinubu ya samu kuri’a 1,271, yayin da Rotimi Amaechi ya samu 316, shi kuwa mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya samu kuri’a 235.
Ragowar sun hada da Gwamnan Jihar Ebonyi, Dave Umahi mai kuri’a 38, Yahaya Bello na Kogi mai 47, tshohon Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu 1, tsohon Gwamnan Zamfara, Ahmed Sani 4, Tunde Bakare 0, Rochas Okorocha 0, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya samu kuri’a 152 sai Gwamnan Kuros Riba, Ben Ayade da ya kare da kuri’a 37.
Takarar Musulmi da Musulmi ta tada kura a APC
Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya zabi Sanata Kashim Shettima, tsohon Gwamnan Jihar Borno, wanda shi ma Musulmi ne, a matsayin abokin takararsa, lamarin da ya harzuka masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da kuma Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).
Sai dai Tinubu, ya kare matsayin nasa na zabar tsohon Shettima a matsayin abokin takararsa a zaben 2023, yana mai cewa ba zai yiwu ya zabi Musulmi da Kirista a lokaci guda ba.
Gabanin bayyana Shettima a matsayin abokin takara, an dai yi ta cece-kuce a kan tsayar da abokan takara da suke kan akidar addini daya.
Da yake zayyana dalilinsa na zabar Shettima, Tinubu ya ce a duk rayuwarsa, babu wata shawara da zai yanke ko wani hukunci da zai zartar game da mabiyansa face ya yi la’akari da kaidojin cancanta, tausayi, mutunci, riko da gaskiya da amana da kuma nagarta.
Tinubu ya kuma ce ya yi tuntuba mai zurfi kan batun zabar abokin takararsa, kuma ya yaba da ta ra’ayoyin jiga-jigan jam’iyyar da abokan siyasa wadanda a cewarsa sun kasance tamkar shi, saboda babu abin da suke hange face makomar Najeriya.
Tinubu ya ce jagoranci nagari da kwarewa da kuma cancanta ya yi la’akari da su wajen zabo abokin takararsa.
Kwankwaso da Peter Obi sun shiga sabbin jam’iyyu don yin takara
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya fice daga Jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar NNPP da ake ganin ya farfado da ita don yin takarar Shugaban Kasa, bayan ya sha fama da rikicin cikin gida a PDP.
’Ya’yan Jam’iyyar PDP sun rika tururuwar barin jam’iyyar suna komawa NNPP, inda a hatta dan takarar Gwamna a Jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2019 a Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana ficewarsa daga PDP zuwa NNPP inda ya ce rashin adalcin jam’iyyar ce ya janyo ficewarsa.
Wadansu na ganin shigar Sanata Kwankwaso da Injiniya Abba Kabir NNPP zai ba jam’iyyar karfin da ake ganin za ta zama barazana ga jam’iyyar APC, akalla a Jihar Kano.
A hannun guda kuwa, shi ma tsohon Gwamnan Jihar Anambra, kuma tsohon dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2019, Peter Obi, ya fice daga PDP inda ya koma jam’iyyar LP.
Peter Obi dai, wanda ya karade jihohi da dama na Najeriya don neman goyon bayan daliget-daliget a yunkurinsa na neman takarar ya fice daga jam’iyyar ne sa’o’i 72 kafin zaben fid-da-gwaninta da aka gudanar a watan Mayu.
Yanzu haka dai ana jiran watan Fabrairun 2023, wanda a nan ne wadannan manyan ‘yan takara; Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso da kuma Peter Obi za su barje gumi a babban zaben da ke kara karatowa.