✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimman abubuwa a makon farko na Gasar Premier ta Ingila

A ranar 16 ga watan da muke ciki ne aka fara Gasar Premier ta Ingila ta bana, inda aka buga wasan farko tsakanin kulob din…

A ranar 16 ga watan da muke ciki ne aka fara Gasar Premier ta Ingila ta bana, inda aka buga wasan farko tsakanin kulob din Manchester United da kuma Swansea City.
Kulob din Swansea City ya samu nasara a kan Manchester United da ci 2-1.
Daga nan sauran wasanni suka biyo baya har zuwa ranar Litinin da aka buga wasan karshe na makon farko na gasar ta bana tsakanin Burnley da Chelsea, inda kulob din Chelsea ya samu nasara a kan Burnley da ci 3-1.
Aminiya ta kawo muku muhimman abubuwan da suka faru a makon farko na gasar ta bana kamar haka:
dan wasan kulob din Swansea City Suu Khi ne ya jefa kwallo ta farko a minti na 28 a lokacin da kulob dinsa ya buga wasa da Manchester United a filin wasa na Old Trafford.
Nathan Dyer daga kulob din Swansea City ne aka fara ba katin gargadi a minti na 25 a lokacin da kulob dinsa ya buga wasa da Manchester United.
Jesse Lingard dan wasan baya na kulob din Manchester United ne aka fara canjawa a gasar ta bana, inda Adnan Januzaj ya canja shi a minti na 23 lokacin da kulob dinsa ya buga wasa da Swansea City.
A yayin wasan tsakanin Manchester United da Swansea City ne dai Wayne Rooney (Manchester United) ya zama dan wasa na farko da ya fara yin kararrawa a gasar ta bana. Ya yi ta a minti na 65.
Lee Cattermole daga kulob din Sunderland ne ya jefa kwallo mafi sauri a lokacin da kulob dinsa ya fafata da kulob din West Brom. Ya jefa kwallon a minti na 5 da fara wasa.
Kyle Naughton daga kulob din Tottenham ne ya zama dan wasa na farko da ya fara jawo bugun fenariti da kuma karbar katin kora a lokacin da kulob dinsa ya kece-raini da kulob din West Ham. Ya jawo bugun fenariti a minti na 27, an ba shi katin kora a minti na 28.
Mark Noble daga kulob din West Ham ne ya fara barar da bugun fenariti a lokacin da kulob dinsa ya buga wasa da Tottenham. Golan Tottenham Hugo Lloris ne ya zama gola na farko da ya kade bugun fenariti a minti na 28 da sakan 10.
Saido Berahino dan wasan kulob din West Brom ne ya fara jefa kwallo ta hanyar bugun fenariti, kuma na farko da ya fara jefa kwallo 2 a gasar ta bana. Ya samu wannan nasarar ne a lokacin da kulob dinsa ya buga wasa da kulob din Sunderland.
A cikin wasannin 10 da aka buga a makon farko na gasar ta bana an jefa kwallaye 26.
A cikin wasanni 10 da aka buga kulob din Arsenal da Liberpool ne suka samu nasara a gida bayan kulob din Arsenal ya ci kulob din Crystal Palace 2 da1, na Liberpool kuma ya samu nasara a kan Southampton da ci 2 da1.
An yi kunne doki a wasanni biyu, wato tsakanin Leicester City da Eberton da kuma West Brom da Sunderland duka da ci 2 da 2.
Kulob-kulob din da suka sha kashi a gida sun hada da Manchester United da Newcastle United da Burnley, kPR da Stoke City da kuma West Ham.
Wadannan kadan daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon farko na gasar premier ta Ingila ta bana ke nan.