✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimman abubuwa a lokacin Babbar Sallah

Abubuwan da ya kamata a rika yi a lokacin Babbar Sallah

Muna taya ku farin ciki da Allah Ya sa muka shaida zagayowar Babba Sallah.

Saboda haka muka yi muku guzurin wasu abubuwa da ya kamata a lizimta a lokacin nan, a takaice:

 • Kabbarori.
 • Jinkirta cin abinci
 • Wankan ranar idi
 • Sanya turare
 • Caba ado
 • Sanya kaya masu launi
 • Halartar sallar idi
 • Babu nafila kafin sallar idi
 • Sauraron hudubar idi
 • Sauya hanyar komawa gida
 • Yanka dabbar layya bayan liman
 • Bude baki naman layya
 • Taya juna murna
 • Ba a azumi a ranar sallah
 • Ayyukan alheri

Duk da yake wadannan abubuwa kan zo a duk shekara, yana da kyau a dan yi karin haske game da su.

 • Kabbarori: Ana so a rika yin kabbarori, musamman bayan sallolin farilla daga sallar asuba ta ranar idi, har a yi sallolin farilla 20.

Kabbarar ita ce: Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar, La ilaha illal Lahu, Allahu Akbar Allahu Akbar walil Lahula hamdu.

 • Wankar idi: Daga cikin ladubban ranar idi akwai yin wankan ibada. Wankan tsarki mutum zai yi domin dacewa da hakan.
 • Jinkirta cin abinci: A babbar sallah ana so mutum ya kame baki kar ya ci komai har sai an sauko daga sallar idi.

Idan mutum zai yi layya an fi son abun da zai fara ci ya zama naman dabbar layyar da ya yanka.

 • Sanya turare: Ana so Musulmi ya fesa turare bayan ya yi wanka a ranar idi domin ya fita yana kanshi.

Amma kuma ba a so mace ta sanya turare idan za ta shiga cikin jama’a.

 • Caba ado: Ranar idi rana ce ado da kwalliyya, shi ya sa ake bukatar Musulmi ya sanya sabbin kaya a ranar, ga mai halin yin haka.

Kayan su kasance kyawawa, wadanda mutum ya fi so, kuma su kasance da tsafta.

Amma mata, ana bukatar su rufe kwalliyarsu da adonsu daga wadanda ba muharramansu ba.

 • Tufafi masu launi: Yayin da ake son sanya fararen kaya a ranar Juma’a, da sallah kuma ana so ne mutum ya sa kaya masu wani kala, ba farare ba.
 • Halartar sallar idi: Maza da mata, manya da kanana da ma masu jinin al’ada ana so su halarci hawan idi.

A kokarta a fita sallar idi da wuri saboda a samu a kintsa kafin isowar liman.

Mata za su kasance ne a bayan sahun maza, su kuma masu jinin al’ada za su ware gefe , sai an kammala sallar.

 • Ba a yin nafila kafin sallar idi: Da an je sai a samu wuri a zauna a jira isowar liman kafin a tayar da Sallah.
 • Sauraron huduba: Bayan idar da sallar idi, sai a jira a saurari hudubar liman cikin natsuwa.

Kuskure ne babba mutum ya yi magana a lokacin da limami ke yin huduba.

Bayan liman ya kammala huduba, idan yana da halin yin layya  yakan yanka dabbar layyarsa a gaban jama’a domin su ma su je su yanka nasu.

Idan kuma ba shi da hali sai ya sanar, ya kuma ba da izinin kowa ya je ya yanka nasa.

 • Sauya hanyar: Abun da ake so shi ne idan mutum zai koma gida sai ya bi ta wata hanya sabanin wacce ya bi a lokacin da zai je filin idi.
 • Yanka dabbar layya: Akan fara yanka dabbar layya ce bayan limamin unguwar da yin layyan yake ya fara yankawa.

Mai yin layya ko da mace ce, shi ake so ya yanka dabbarsa, amma ana wakilci.

Sai dai duk wanda ya yanka dabbarsa kafin liman to layyarsa ba ta yi ba.

Mazauna yankunan da babu masallacin idi kuma, za su iya yanka dabbobinsu bayan sun samu labarin cewa limami ya yanka, ko kuma bayan hatsi.

Ana dakatar da yanka dabbar ne idan magariba ta yi.

Washegarin ranar idi, har zuwa kwana uku bayan ranar idi duk za a iya ci gaba da yin layya daga hantsi har zuwa Magariba.

 • Bude baki da naman layya: Ga wanda ya yi layya an fi so abin da zai fara ci a ranar babbar Sallah ya kasance daga naman dabbar layyar.
 • Yi wa juna murna: A ranakun sallah ana so Musulmai su rika taya juna murnar arzikin ganin lokacin da kuma addu’o’i na alheri.
 • Ba a azumi a ranakun yanka: Ranar sallah rana ce ta ci da sha kuma Allah na fushi da duk wanda ke yin azumi a ranar idi.

Kazalika ba a yin azumi a ranakun layya, wato kwanaki uku da ke biye da ranar babbar sallah.

 • Ayyukan alheri: A yawaita bayar da kyauta, musamman ga mabukata da kananan yara. A sadar da zumunci, a kai ziyara sannan a gode wa Allah da Ya sa muka ga sallar.

Mulahaza:

Tabbatar da cewa kana sanye da takunkumin COVID-19 tare da kiyaye matakan kariya a kowane lokaci, muddin za ka shiga cikin jama’a.

A kiyaye dokokin hanya da na sauran hukumomi a ko yaushe.

A rika lura da kananan yara a kuma ba wa jami’an tsaro hadin kai.