✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muhimman abubawa game da Marigayi Buruji Kashamu

Za ku so ku san wadannan abubuwa a kan Marigayi Sanata Buruji Kashamu

A ranar Asabar Allah Ya karbi ran tsohon dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Ogun ta Gabas, Sanata Buruji Kashamu  bayan ya yi fama da cutar COVID-19.

Abokin marigayin kana tsohon dan Majalisar daga Jihar Bayelsa, Sanata Murray Bruce ne ya sanar da mutuwar a shafinsa na sada zumunta.

Ga wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da Sanata Buruji Kashamu da Aminiya ta kawo muku:

  • An haifi Sanata Buruji Kashamu a Jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya a Shekarar 1958.
  • Ya fara karatun firamare a makarantar Ansaru da ke garin Ijebu Igbo a Jihar sannan ya koma makarantar St. John a Legas wadda ya gama a shekarar 1972.
  • Ya ci gaba da karatu a ajujuwa na musamman da yammaci a Kwalejin Igobi, inda ya hada aiki da karatun.
  • Daga nan ya tafi kasar Ingila ya yi kwasakwasai a fannin kasuwanci a Kwalejin Pitman da ke birnin London.
  • Jami’ar Diploma-mill Cambridge da ke Massachusetts, wacce ba a tantance ta ba, ta ba shi shaidar digirin digirgir, a wani biki da aka yi a sirrance a Legas.
  • Mamacin daya ne daga cikin jigajigan jam’iyar adawa ta PDP a jihar Ogun, kana shi ne dan takarar gwamnan jihar na jam’iyar a zaben shekarar 2019.
  • An taba korar sa daga jam’ iyar ta PDP a shekarar 2018 amma wata Babbar Kotu a Abuja ta soke korar a watan Oktoban 2018.
  • A shekarar 1998 an kama shi a kasar Birtaniya bisa zargin  badakalar safarar miyagun kwayoyi bayan da aka same shi da kokarin shiga kasar da Dalar Amurka 230,000.
  • A sheakar 2003 aka sake shi, bayan wata  kotu ta wanke shi.