Gwamnan Jihar Borno, Farfsa Babagana Umara Zulum, ya nuna “matukar” damuwa kan yadda mayakan ISWAP ke karuwa a wasu sassan jihar, lamarin da ya sa ya yi kira da a tashi tsaye a dauki matakan gaggawa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da Kwamitin Majalisar Dattawa da ke kula da sha’anin sojin kasar da ya ziyarce shi a ranar Laraba a Maiduguri.
- ‘Na dauki ci da sayar da sassan jikin mutane a matsayin al’ada’
- Ina dan wasan da ya zura kwallon da Najeriya ta lashe AFCON 2013, Sunday Mba, yake?
Yayin da yake yabawa gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da hukumomin tsaro bisa nasarorin da aka samu a Borno, Zulum ya ce ya damu matuka game da karuwar mayakan ISWAP a sassan jihar, musamman daga bangaren kudanci, inda ya kara da gargadin cewa bangaren na ISWAP sun fi na Boko Haram karfi da kuma makamai.
Gwamnan ya koka kan cewar idan ba a gaggauta daukar mataki ba, barzanar na iya zama illa ba ga mutanen Arewa maso Gabashin Najeriya kadai ba, har ma da kasa baki daya.
“Maganar gaskiya ita ce, ya zama dole mu dauki mataki a kan mayakan ISWAP a Jihar Borno, idan muka ki fatattakar su, ta yi wu su zama matsala ba ga yankin arewa maso gabas kadai ba, har ma da daukacin Najeriya.”
Farfesa Zulum ya kara da cewa, “mayakan ISWAP na da makamai kuma a shirye suke sannan suna da basira fiye da mayakan Boko Haram kuma suna karuwa akai-akai, dalilin kenan da ya sa ya kamata a fatattake su.”
Gwamnan ya kuma mika godiya ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da dakarun Najeriya da masu ayyukan sa-kai saboda irin taimakon da suke bayar wa.
“Jihar Borno na ganin dawowar zaman lafiya a hankali wanda hakan ya yi wu ne saboda taimako da gwamnatin tarayya ta ba mu.
“Sannan shugabannin jami’an tsaro su ma suna ba da nasu hadin kan. A takaice, shugabannin rundunonin soji su ma suna ba da nasu taimakon,” a cewar Zulum.
Sai dai gwamnan ya nuna damuwa kan yadda mayakan ISWAP suke barazanar mayar da hannun agogo baya kan nasarorin da aka samu.
A gefe guda kuma gwamnan har ila yau ya ce mika wuya da daruruwan mayakan Boko Haram suka yi a kwanan nan, ya sa ana samun zaman lafiya musamman a yankunan da ake harkokin noma.
Gabanin jawabin na gwamna Zulum, Sanata Ndume wanda ke zaman jagora ya bayyana cewa kwamitin ya kai ziyarar ne don nuna godiya ga gwamnatin jihar Borno kan yadda take ba sojoji hadin kai da taimako, batun da su ma dakarun kasar suka jaddada a baya.