Shugaban Kungiyar Masu Sayar da Kaji ta Abuja Alhaji Danladi Hashimu Maikaji ya bukaci ya yaba wa al’ummar kasar nan kan sake zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda ya bukaci su tallafa masa da addu’a don ya samu nasarar dora kasar nan a kan turbar ci gaba.
Alhaji Danladi Maikaji ya yi wannan kira ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya, inda ya ce hakika masu zabe a Najeriya sun yi abin da ya kamata na sake ba Shugaba Buhari dama ya dora daga inda yake. “Talakawa masu zabe sun cancanci yabo da godiya, ’yan Najeriya sun cancanci jinjina, haka magoya bayan Jam’iyyar APC sun cancanci yabo kan yadda suka fito kwansu da kwarkwata suka zabi ’yan takarar APC ta koma gadon mulki. Amma ina kira ga jama’ar kasar nan su kara wa shugabannin nan da addu’a a kokarinsu na gyaran kasar nan,” inji shi.
Shugaban ya kuma yi kira ga zababbun shugabannin cewa su kuma su yi kokari su nuna shugabanci nagari wajen kyautata rayuwar jama’ar da suka sadaukar da kansu suka zabe su. “Ya kamata wadanda aka zaba su tuna cewa wadanda suka zabe su wadansu sun sadaukar da dukiya da lokaci da komai nasu don ganin sun kai su gadon mulki. Don haka mu magoya bayan Jam’iyyar APC muna fata za sub a marada kunya su tsaya su gudanar da abubuwan da za su kyautata rayuwar jama’a, su tallafa wa marasa karfi su tallafa wa’yan kasuwa da manoma da masu sana’o’i su rika biyan ma’aikata da ’yan fansho hakkokinsu a kan lokaci, su kula da wadanda suka zabe su. Yin haka ne zai sa mu rika tutiyar cewa ba mu yi zaben tumun dare ba,” inji Danldai Maikaji.
Ya yi fatan Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa Adams Oshiomhole da shugabanin jam’iyyar a matakan jihohi za su fito da hanyoyin kyautata wa ’ya’yan jam’iyyar tun daga sama har unguwanni domin rike jam’iyyar ta zauna da kafafunta. Ya ce irin haka babbar jam’iyyar adawa ta PDP take yi shi ya sa har yanzu ake jin motsinta.
Sai kuma ya yi fatan hukumomin tsaro da sauran masu ruwa-da-tsaki za su tashi tsaye don magance matsalar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a kasar nan, domin sai da zaman lafiya za a iya gudanar da ayyukan ci gaba.
Sai kuma ya mika godiya ga ’ya’yan kungiyarsu kan yadda suka bayar da goyon baya tare da sake zaben jam’iyyar APC a matakai daban-daban a sassan kasar nan.