✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mu Sha Dariya: Wani Buzu

Ai na baro maigida a Kano.

Wani Buzu ne ya je Kano ci-rani, ya sauka gidan wani attajiri, wanda ya rike shi da mutunci.

Da zai koma garinsu sai mutumin ya yi masa sha tara ta arziki.

Da ya isa kauyensu, yana shiga gida sai matansa suka rugo da murna, suka tarbe shi, suna cewa: “Oyoyo ga maigida, oyoyo ga maigida!”

Shi kuwa sai ya ce: “Maigida nake ko dai dan iska, ai na baro maigida a Kano.”

A nufinsa shi bai da dukiya, don haka dan iska ne shi, maigidansa na Kano.

Daga Ibrahim Hashim Kaya, Asaba Jihar Delta