✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mu Sha Dariya: Ko gida Halima ake kira na!

Kin yi sa’a, ban taba Halima.

Wani Bahadeje ne yake yi wa matarsa kurin shi jarumi ne. Sai tafiya ta kama su, ya yi shirin yaki, suna tafiya cikin daji sai ga dan fashi.

Ya yi masu tsawa suka tsaya cik. Da ya zo sai ya tambayi matar sunanta, ta ce Halima.

Dan fashin ya ce: “Kin yi sa’a, ban taba Halima, domin sunan mahaifiyata ce.”

Ya juya wurin mijin ya ce: “Kai yaya sunanka?”

Sai ya ce: “Wallahi, ni ma ko gida Halima ake kira na kuma ka tambayi matata.”

Daga Mudassir Maishayi Ningi, 08169139393