Wani dan sanda ne ya tsare direba inda ya fara yi masa tambayoyi kamar dai yadda jami’ai suka saba yi wa masu ababen hawa a kan hanya.
Ga yadda tattaunawarsu ta kasance:
Dan sanda: “Ina takardun motarka?”
Direba: “Ga su nan.”
Dan sanda: “Ina lasisinka?”
Direba: “Ga shi nan.” (Komai aka tambayi direba yana da shi, dan sanda ya gaza kama shi da laifi).
Dan sanda: “To wa ya ce ka rika tafiya kai daya a mota, idan wani abu ya same ka wa zai mai da ka gida?”
Direba: “Manzon Allah (SAW) ya ba mu wata addu’a, a duk lokacin da zan yi tafiya, idan na karanta ta, mala’iku dubu suna tare da ni.”
Dan sanda: “Mala’iku dubu a karamar mota? To ka yi obalodi, mu tafi ofis, na kama ka!”
Daga Isma’il Lawal Gambo