✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu Sha Dariya: Kauce nan dodo zai wuce!

Sai aka ajiye furar a dakin, aka tafi aka bar shi.

Wani mutum ne mai kawaici ya je gai da surukansa, sai aka kawo masa fura a kwarya.

Ya ce ya koshi, aka yi juyin duniyar nan da shi, ya ce ya koshi.

Sai aka ajiye furar a dakin, aka tafi aka bar shi.

Bayan wani lokaci sai ya fara tunanin yadda zai sha furar ba a gane ba.

Ya ga cewa idan ya sa ludayi, ko ya karkata kokon ya sha, za a gane; sai ya ce bari ya tsoma baki.

Ya fara sha ke nan sai hannunsa ya goce, fura kuwa ta yi masa kaca-kaca da fuska.

Kunya ta kama shi ya fito bakin kofa zai bar gidan sai ya ci karo da surukan nasa.

Sai ya ce masu: “Ku kauce nan dodo zai wuce!”