Wani Bafulatani ne ma’abocin sauraron rediyo, kowane lokaci za a same shi ya kasa kunne yana sauraron labarai gami da kade-kade.
Ana cikin wannan hali sai wannan babbar rediyo ta samu matsala ta lalace.
Ya yi tunanin ko batirin rediyon ne ya mutu sai ya sayo sababbi ya sanya amma shiru ba wani motsi.
A haka ya hakura, ya je ya samu wani wuri a cikin dakinsa ya rataye radiyon nan, kafin ranar kasuwa ta zagayo ya kai ta a gyara masa.
Ashe hanyar wasu manyan beraye ce ya sa rediyon tasa.
Ko da ganin haka sai berayen nan suka rika shiga ciki suka yi gida.
Wata daga cikinsu har ta haihu, duk abin da ke faruwa bai sani ba.
Ranar kasuwa na zagayowa, dan Fillo ya sun gumi rediyo sai wurin mai gyara.
Yana zuwa ya ci sa’a ba layi a wurin mai gyaran.
Mai gyara ya kama rediyo ya kwance. Yana budewa sai ga wani katon bera ya fito a guje.
Ganin haka Bafulatani ya sabi sanda ya bi beran nan a guje, yana fadin cewa: “Jama’a ku tare mini, ga mai ba da labarai zai gudu.”
Daga Nura Suleja, Neja