✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mu Sha Dariya: Amma ka hadu

Wani saurayi ne ya je dandalin shakatawa sai ya ga wata budurwa ita kadai a zaune.

Wani saurayi ne ya je dandalin shakatawa sai ya ga wata budurwa ita kadai a zaune.

Ya karasa wajenta ya yi mata sallama ta amsa, sai ya ce: “Kamar na so in san ki a ABU Zariya.”

Ta ce: “Ni ce, don ina karatu a can ne, ina mataki na 300. Kai fa?”

Sai ya ce mata: “Ni ma ina karatu a can, ina mataki na 900, ina jira ne in karasa zuwa mataki na 1500, in amshi takarduna, in fara neman aiki.”

Ta ce wane kwas yake nazarta, sai ya ce mata: “Ina karanta Islamic Engineering ne.”

Ta ce masa wace firamare ya yi, sai ya ce mata: “Ai na yi Primary Election ne tukun, kafin in tafi Secondary Election, daga nan na yi BUK, sannan na zo ABU, Zariya. Kin ji yadda abin ya yi ta gudanuwa zuwa yanzu.”

Sai ta ce masa: “Kai, lallai amma ka hadu.”

Daga Yakubu Adamu Ningi, 09021109997