✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

  Bakanuwa da tuffa Wata Bakanuwa ce ta je Saudiya, sai ta ga wasu suna shan tuffa, ita ma sai ta saya. Ta kai hakoranta…

 

Bakanuwa da tuffa

Wata Bakanuwa ce ta je Saudiya, sai ta ga wasu suna shan tuffa, ita ma sai ta saya. Ta kai hakoranta da karfi sai ta ji sun nutse a ciki kuma ga ruwansa ya biyo hannunta. Mamaki ya kama ta, ta ce: “Kai, goriba sai kasar Saudiya, ga mai zaki ga taushi, ashe a Kano cutar mu ake yi.”

Daga M. A. Faruk Sakkwato 08036029098

Miji da mata

Wani maigidane bayan ya dawo gidansa daga wajen aiki, ya zauna sai matarsa ta zo ta zauna suka fara hira irin ta miji da mata. Ga yadda hirar tasu ta kasance: Mata: “Maigida, sannu da zuwa.” Miji: “Yawwa uwargida, ya yaran?” Mata: “Lafiyarsu kalau.” Miji: “Allah Ya yi miki albarka.” Mata: “Amin, rabin raina.” Miji: “Uwargida kin ji wani labari da na ji yau?” Mata: “A’a sai ka fada.” Miji: “Yanzu nake jin labarin cewa maigari ya ba da sanarwar cewa duk mai mace daya an ba shi nan da kwana uku ya kara aure, idan ba haka ba za a kashe shi.” Mata: “Alhamdu lillah! Ka ga maigida shi ke nan za ka yi mutuwar shahada.” (Tana nufin gara a kashe shi da a ce ya kara aure, domin ba ta son kishiya).

Daga Isah Ramin Hudu, Hadeja 08060353382

Damun fura

Wani Bahadeje ne ya je wurin masu sayar da fura da nono, ya ce: “A ba ni gayar fura ta Naira ashirin.” Da aka ba shi sai ya sanya a baki ya cinye. Ya sake cewa: “A ba ni sukari na Naira goma.” Da aka ba shi sai ya shanye. Ya kara cewa a ba shi nono na Naira ashirin. Bayan an ba shi sai ya shanye. Yana shanyewa sai ya kama kugu yana juyawa. Aka ce masa me yake yi sai ya ce: “Dama furar nake yi!”

Daga Hajiya Loliya, 08162472249

Direba da ustaz

Wani direba ne ya kira wani ustaz domin su tafi aikin mota tare. Sun fita tun safe suna aiki har rana ta yi zafi. Bayan an cika mota da fasinja sai ustaz ya ce su kawo kudin mota. Da aka fara bashi kudin, sai ya shafa aljihu domin ya ba wani mutum canji sai ya ji babu kudin da suka yini suna aiki a aljihun, wani ya sace. Nan da nan sai ya fara kabbara da karfi, ya ce: “Allahu akbar, wani ya cuci kansa!” Direba ya juyo ya ce: “Ustaz, yaya aka yi ne?” Shi kuwa ya ce: “Ai duk cinikin da muka yi yau, wani ya sace su.” Direba ya ce: “Ka ce ya cuci kansa ko dai ya cuce mu?”

Daga Khalil Muhammad, 08031908918