✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Tun a farkon yakin aka kashe ni! Malamin makarantar su Shehu ne ya shiga aji domin yi wa dalibai jarrabawar gwaji. Ya tambaye su cewa:…

Tun a farkon yakin aka kashe ni!

Malamin makarantar su Shehu ne ya shiga aji domin yi wa dalibai jarrabawar gwaji. Ya tambaye su cewa: “Ka dauka kai soja ne da kuka dawo daga filin yaki, rubuta abubuwan da suka faru lokacin da kuke filin daga.” Aka gama malamin ya fara tattara takardun dalibai, sai ya ga takardar Shehu bai rubuta komai ba; sai ya tambaye shi dalilin da ya sa bai rubuta komai ba. Shehu ya amsa da cewa: “Ai tun a farkon yakin aka kashe ni.”

Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011

 

 

Maganin mutuwa

Wani yaro ne ya ce da malaminsa ya fada masa maganin mutuwa. Sai malamin ya ce masa: “Ka karanta A.B.C.D har zuwa Z kafa dubu daya, ka tofa a ruwa ka shanye kuma ka shafe jikinka da shi. Idan ka yi haka ba za ka mutu ba sai ranar da kwananka ya kare.”

Daga Haiman Khan Ra’is, 08185819176

 

 

Kukan kauna

Wani saurayi ne da budurwarsa suna hira, sai ta ce masa tana jin kwadayi, ya je ya sayo mata gasasshen nama. Bayan ya fita sai ya duba aljihunsa, ya ga Naira hamsin kadai yake da ita. Sai ya ce wa mai nama: “Ka ba ni nama na Naira hamsin amma ka yanka mini albasa da yawa.” Aka yanka masa ya kawo mata, dama an dauke wuta, akwai duhu, sai ya tura mata naman, shi kuma ya kama cin albasa. Nan fa idanunsa suka tara hawaye. Bayan lokaci aka kawo wuta, lokacin kuma sun gama cinye naman. Yarinya ta ga idon saurayinta na zubar hawaye, sai ta tambaye shi dalilin da yake kuka. Sai ya ce: “Tsananin kaunarki ce ta sanya ni kuka!”

Daga Dan Fagge, 08058009561

 

Kunna talabijin

Wani Bafulatani ne ya je birni ya ga talabijin kuma ya burge shi. Don ya burge ’yan uwansa a kauye sai ya saya ya biya kudi. Mai kanti ya ce masa: “Ai da ka je gida ka hada masa wuta, ka kunna sai kallo kawai!” Shi kuwa Bafulatani cikin sauri ya dauki akwatin talabijin, yana zuwa gida sai ya tattara karmami da yayi, ya rufe talabijin, ya banka masa wuta. Ya koma gefe daya yana kallon ikon Allah.

Daga Nafisa Basiru Sadi, 07037902893