✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Sauro da dansa Wani sauro ne ya fara koya wa dansa tashi, har ya fara kwarewa. Ran nan sai uban ya ce masa: “Ya kamata…

Sauro da dansa

Wani sauro ne ya fara koya wa dansa tashi, har ya fara kwarewa. Ran nan sai uban ya ce masa: “Ya kamata yau ka tashi kai kadai, domin in ga kwarewarka.” Dan sauron nan ya bude fiffikensa ya tashi sama, ya yi shawagi. Bayan ya dawo, ya sauka, sai uban ya tambaye shi: “Shin yaya ka ji lokacin da ka tashi?” Cikin farin ciki dan sauron ya gaya wa babansa cewa: “Wato abin da ya fi burge ni, shi ne irin yadda na ga duk inda na wuce mutane na yi mini tafi.” Uban ya kalle shi ya yi murmushi ya ce: “ Yaro, ai ba tafi suke maka ba, kashe ka suke so su yi.”

Daga Fatuhu Mustapha

 

Ka tabbata a nan aka kashe Murtala?

Wani sabon malami ne aka kawo shi wata makarantar sakandare, domin ya koyar da Tarihi. Shigarsa aji ke da wuya  sai ya ce wa wani dalibin:  “Tashi tsaye, shin wa ya kashe Murtala Ramat Muhammad?” Dalibin ya ce:  “Malam, ban sani ba.” Sai ya tambayi dalibi na biyu, shi kuma sai ya ce: “Malam, ranar da aka kashe shi ban zo makaranta ba.” Dalibi na uku kuma ya ce: “Wallahi ni sabon zuwa ne makarantar nan.” Malamin ransa ya baci, sai ya kirawo shugaban makarantar ya gaya masa abin da ya faru, sai shugaban makaranta ya tambayi ’yan ajin baki dayansu, suka ce ba su sani ba. Sai shugaban makarantar ya juyo, ya ce da malamin: “Kai malam, ka tabbata a nan ajin aka kashe Murtala Ramat Muhammad?”

Daga Malam Babaji Na Ummi Hadeja, 08108484300

 

Tashi ka bi su!

Wani Bakano ne ya ji ana zanga-zanga a jami’ar da dansa yake sai ya kira shi ya ce: Musa, kana ina ne yanzu haka? Yaro: Baba, ina dakin makaranta a kwance. Baba: Madalla! Na ji an ce dalibai suna zanga-zanga da kone-kone a makarantarku, to wallahi kada ka kuskura ka bi su ka san dai irin tarbiyyar gidanku. Yaro: Idan Allah Ya yarda ba zan bisu ba Baba.” Baba: Yauwa dan arziki sai an jima. Bayan minti 15, ya sake kiran yaron ya ce: “Mene ne dalilin zanga-zangar? Yaro: Wai saboda hukumar makaranta ta kara mana kudin makaranta daga Naira dubu 30 zuwa Naira dubu 300. Baba: Iye! Yanzu kana ina? Yaro: Ina kwance a daki. Baba: Ashe kai mahaukaci ne? Tashi ka bi su!

Daga Malam Babaji Na-Ummi Hadeja, 08108484300

 

Na dagula

Wani kuturu ne ya je sayen garin kwaki a shagon wani Ibo, sai ya sa dungunsa ya debi kadan don dandanawa. Sai Ibon ya kwashe daidai wurin da ya sa hannu ya zubar. Sai haushi ya kama kuturu, sai ya tura dungun hannun duka cikin kwanon garin, ya ce “Na dagula! Na dagula!”

Sayyada Fatima Muhammad Galadima Bichi