✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Tashi ka bi su! Wani Bakano ne ya kira dansa da yake karatu a jami’a. Ga yanda hirarsu ta kasance: Baba: Musa, kana ina ne…

Tashi ka bi su!

Wani Bakano ne ya kira dansa da yake karatu a jami’a. Ga yanda hirarsu ta kasance: Baba: Musa, kana ina ne yanzu haka? Yaro: Baba, ina dakin makaranta a kwance. Baba: Madalla! Na ji ana cewa dalibai suna ta zanga-zanga da kone-kone a makarantarku, to wallahi kada ka kuskura ka bi su ka san dai irin tarbiyyar gidanku. Yaro: Idan Allah Ya yarda ba zan bi su ba baba.” Baba: Yauwa dan arziki sai an jima. Bayan minti 15, ya sake kiran yaron ya ce da shi: “Wai mene ne dalilin yin wannan zanga-zangar? Yaro: Wai saboda hukumar makaranta ta kara mana kudin makaranta daga Naira dubu 30 zuwa Naira dubu 300. Baba: Iye! Yanzu kana ina? Yaro: Ina kwance a daki. Baba: Ashe kai mahaukaci ne? Tashi ka bi su!

Daga Malam Babaji Na Ummi Hadeja, 08108484300

 

Na dagula! Na dagula!!

Wani kuturu ne ya je sayen garin kwaki wajen wani Ibo, sai ya sa dungun hannunsa ya debi kadan da nufin dandanawa. Sai Ibon ya kwashe daidai wajen da ya sa hannu ya zubar. Sai haushi ya kama kuturu, sai ya tura dungun hannun duka cikin buhun garin, ya ce “Na dagula! Na dagula!!”

Sayyada Fatima Muhammad Galadima Bichi

 

Banufe da wanzami

Wani wanzami ne yana yi wa Banufe aski sai Banufen ya saki tusa mai kara ‘buuurrrrrr!’ a zatonsa wanzami bai ji ba saboda karar kida da ke tashi a shagon askin. Shi kuwa wanzami sai ya ce: “Shin karar me nake ji haka? Sai Banufe ya ce: “Iskar bazara ce.” Wanzami, cikin mamaki ya ce: “Idan dai ko wannan iskar bazara ce, to kuwa ashe bana za a yi ruwan kashi ke nan!”

Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011

 

Fesa sama-sama!

Wani yaro ne aka sayo musu maganin sauro na fesawa, sai mahaifiyarsa ta ce ya fesa sama-sama a dakin. Tana nufin kada ya fesa da yawa. Shi kuma saboda rashin Hausa sai ya daga gwangwanin maganin ya rika fesawa a saman dakin sai da ya kare maganin kaf. Da mahaifiyar ta ji warin maganin ya yi yawa, sai ta tambaye shi dalili, sai ya ce: “Ai ke kika ce in fesa sama-sama, ni kuma na daga sama na feshe shi duka!

Daga Khadija Ahmad Babale, 08063625937