Ba duka ba zagi
Wata rana ne wani Buza ya dawo gidansa sai ya kama wani kwarto. Sai kwarto ya fara yi masa magiya, cewa don Allah kada ya buge shi. Shi kuwa Buzu sai ya ce: “Kai walla, ba duka ba zagi, ki kwanta kawai ta rama .”
Wa ka yi ma wa?
Wata rana ne wani Bamaguje ya kiwata wani sa ya zama babban bajimi. Ran nan ya dawo daga gona sai ya tarar da shi ya yi mushe, sai ya ce: “Haba bajimi, wa ka yi ma wa? Kai ka ciki za mu yi.”
Walakiri akwai zuciya
Wani Bafulatani ne babansa ya rasu, sai ya je ya samo katuwar sanda ya sanya cikin kabarin, aka rufe tare da mahaifin nasa. Bayan an gama jana’iza sai ya kalli kabarin ya ce: “Yau fa za a yi ta, Walakiri akwai zuciya, Baffa ma haka!”
Labarai daga Isma’il Maishadda, 07032775928
Karambanin saurayi
Wani saurayi ne ya je wajen budurwarsa, suna cikin hira sai NEPA suka kawo wuta sai ya tambaye ta cewa: “Yaya na ga ko’ina da wuta amma ban da gidanku?” Sai ta ce ai lokacin ana ruwan sama sh ine iska ta tsinke wayarsu. Sai ya ce to me ya sa ba su kira ’yan NEPA sun gyara ba? Sai ta ce, wallahi mun kira su sun ce za su zo, ga shi yau har kwana biyu shiru. Sai ya ce mata ta shiga gida ta sa yara su fito masa da tsani da filaya. Sai ta ce: “Haba, kawai ka bar shi za a gyara, ka ga ba aikinka ba ne.” Sai ya ce haba masoyiyata, ai abin duk buge ne!” Aka fito masa da tsani da sauran kayan aiki, ya hau falwaya ya fara aiki. Can zuwa wani dan lokaci sai budurwarsa ta ji ya kwarma ihu hade da kara. Wayar wuta ta jawo shi kasa, ya fado cikin kwata a sume. Bayan ya farfado, ya tashi zaune, yana daga kansa sai ya ga budurwarsa da iyayenta da yaran gidan gaba daya da sauran yaran unguwa suna yi masa sannu. Can sai aka ji wata karamar yarinya kanwar budurwarsa ta ce: “La! Anti, saurayinki ya yi kashi a wando!”
Daga Musa Umar Foreber Gashuwa, 08060110011