✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Kukan kauna Wani saurayi ne da budurwarsa suna hira, sai ta ce masa tana jin kwadayi, ya je ya sayo mata gasasshen nama. Bayan ya…

Kukan kauna

Wani saurayi ne da budurwarsa suna hira, sai ta ce masa tana jin kwadayi, ya je ya sayo mata gasasshen nama. Bayan ya fita sai ya duba aljihunsa, ya ga Naira hamsin kadai yake da ita. Sai ya ce wa mai nama: “Ka ba ni nama na Naira hamsin amma ka yanka mini albasa da yawa.” Aka yanka masa ya kawo mata, dama an dauke wuta, akwai duhu, sai ya tura mata naman, shi kuma ya kama cin albasa. Nan fa idanunsa suka tara hawaye. Bayan lokaci aka kawo wuta, lokacin kuma suka gama cinye nama. Yarinya ta ga idon saurayinta na zubar hawaye, ta tambaye shi dalilin da yake kuka. Shi kuwa sai ya ce: “Tsananin kaunarki ce ta sanya ni kuka!”

Daga dan Fagge, 08058009561

 

Wani Bafulatani

Wani Bafulatani ne da Babarbare suna cikin sahun Sallar Juma’a, liman yana cikin huduba sai tusa ta kubuce wa Bafulatani har ma ta yi kara mutane sun ji, sai suka kalli bangaren da tusa ta fito. Bafulatani ya yi tsuru-tsuru, Babarbare da yake kusa da shi sai ya kura masa ido, alamar ya gane shi ya yi tusar. Da Bafulatani ya ga zai tona masa asiri sai ya kalli Babarbare ya ce masa: “Yau ai sai ka tashi ka je ka sake alwala.”

Daga Adamu Mahmud Dogonjeji, 08057631302

 

Bakar magana

Wasu mutane ne su uku suna zaune sai ga mai sayar da nama zai wuce. Suka kira shi domin su saya, daya ya ce a yanka masa na Naira hamsin, shi ma dayan ya ce a yanka masa na hamsin. Sai aka tambayi dayan shi kuma na nawa za a yanka masa, sai ya ce: “Ni likita ya hana ni cin nama amma dai dan yanko mani kadan in dandana.” Mai nama ya yanka masa, ya saka a baki ya ji dadi, sai ya ce masa: “Yanko mani na Naira ashirin.” Jin haka sai mai nama ya ce: “dauko baro!”

Daga Aminu M. Ibrahim, 09034793420

 

 

Kar nake ganin ka

Wani dan sanda ne ya kama kugun dan sholisho a kamen da suka je, sai ya lura akwai kudi a aljihun dan sholin. Cikin dabara sai ya zura hannu zai zaro kudin, ashe dan sholisho ya ankara, sai ya fashe da dariya yana kallon dan sanda; ya ce: “Kai barawo, kar nake ganinka dan kwana-kwana.” dan sanda ya ji haushi jin an ce masa dan kwana-kwana, ya zabga masa mari. dan sholi ya yi taga-taga ya dawo yana duban dan sandan sosai, ya ce: “Au sori, izi; ai ban ga igiyar ba sai yanzu.”

Daga Halima Shata Katsina (anti Dubu), 08131014066