✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Talauci ya yi rana Wani Bafulatani ne zai hau mota a tasha sai kudinsa ba su cika ba sai aka ki yi masa ragi. A…

Talauci ya yi rana

Wani Bafulatani ne zai hau mota a tasha sai kudinsa ba su cika ba sai aka ki yi masa ragi. A nan aka bar shi a tasha, mota ta tafi. Motar na cikin tafiya sai ta yi hatsari, wasu suka mutu wasu suka ji ciwo. Da aka dawo da su, Bafulatani ya tambayi abin da ya faru sai aka fada masa yadda hadarin ya faru. Budar bakin gogan naku ke da wuya sai ya ce: “Kan uba! Aradu yau talauci ya yi rana!!”

Daga Mustapha Bashir Yahuza Malumfashi

 

Kaza da akuya

Wata rana kaza da akuya sun fito yawo bakin titi, suna cikin tafiya sai wani mai mota ya taho da gudu ya fantsala musu ruwa. Sai kazar nan ta ce: “Mtss! Mutane haka suke tuki sai ka ce awakai.” Sai akuyar nan ta ce: Hhmm! Shi ya sa suke mutuwa kamar kaji.”

Daga Alhassan K. Idris Kafin Hausa, 08062936841

 

Ajiyar daji

Wani Bakatsine ne ya ci gasar MTN har Naira milliyan 10. Saboda kada mutane su san yana da wannan kudin, sai ya yanke shawarar kin ajiyewa a gida ko banki. Don haka sai ya tafi daji, ya samu gindin wata bishiya a cikin duhuwa, inda ba sosai mutane ke zuwa wajen ba, ya tona ya binne wannan kudin. Amma sai ya debi wani bangare na kudin ya je ya yi bisa domin tafiya yawon shakatawa zuwa Indiya. Amma kafin ya bar wannan bishiya sai da ya samu waya, ya dauki hoton bishiyar nan don gudun mantuwa. Bayan ya je Indiya, ya sauka a wani otel tsawon sati daya. Rannan yana kwance a daki, sai ya dauko wayar nan, yana duba hoton bishiyar nan da ya binne kudinsa. Yana cikin dubawa, sai ya ga saman bishiyar nan ashe akwai wani mutum yana kallon duk abin nan da ya yi.

Daga Isah Ramin Hudu, Hadeja 08060353382

 

Basakkwace

Wani Basakkwace ne da azumi yana narkar abinci da Asuba sai wani abokin zamansa ya ce: “Kai dan Sakkwato, an kira Assalatu!” Sai ya ce: “Asalatu ehona, sai na ji warabbana.”

 

Saurayi da budurwa

Wata hadaddiyar budurwa ce ta tsaya a kofar gida, sai ga wani saurayi ya zo wucewa, sai ya tsaya tun daga nesa yana kallon ta. Ya lura da cewa ashe ita ma kallon shi take yi, kawai sai ya canja tafiya, ya nufi wajenta. Yana isa gare ta sai ya ce mata: “Sannuki kyakkyawa, daman na zo zan wuce ne sai na ga kina kallona, don haka tun da mun aminta da juna ya za a yi ke nan?” Sai budurwar nan ta fashe da dariya ta ce: “Ba wani abu ba ne ya sa nake kallon ka, wallahi ka yi mini kama da wani biri da ya tsinke ya gudu daga gun mai shi, dazu a kasuwa.

Daga Umar Adamu Isah, 08064385252