✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

MU SHA DARIYA

Gasar gudu Wani matashi ne ya saba da gudu a babur, rannan ya tafi gun aiki, inda ya kai kilomita 25. Ya yi tafiyar da…

Gasar gudu

Wani matashi ne ya saba da gudu a babur, rannan ya tafi gun aiki, inda ya kai kilomita 25. Ya yi tafiyar da ta kai kilomita 23, saura kilomita biyu kawai ya isa, kawai sai suka yi kiliya da wani matashi, shi ma yana tika gudu a nasa babur din. Yana ganin wannann matashi da yake gudu, kawai sai ya yi kwana ya bi shi. Da wancan ya waigo ya ga an biyo shi da gudu, sai ya kara wuta, domin kuwa bai son a wuce shi. Nan fa suka runtuma, suka yi ta gasar tsere a tsakaninsu. Sai da suka ci kilomita 20, sannan ya samu wuce shi, daga nan ya juyo domin tafiya wajen aikinsa. Ya ce: “Haba, ai da ban wuce shi ba, sai ya yi ta kurin shi mai gudu ne.”

Sunusi Uban Kulob Garko Kano 07038766018

 

Saki ko duka?

Wani maigida ne suka samu sabani da matarsa, a maimakon ya yi mata nasiha, kawai sai ya fara dukanta. Yana cikin dukan nata can sai ga abokinsa ya zo, ya ga abin da ke faruwa. A nan ya dakatar da maigidan daga dukan da yake yi wa matar, ya kuma tambaye shi abin da ya faru. A nan ne maigidan ya kwashe labari ya fada masa, sai abokin ya ce: “To kai in ban da kai wa yake dukan mata? Tun dai bata maka rai take yi, sai ka auro mata abokiyar zama.” Matar tana jin abin da abokin nan ya fada, nan take sai ta ce: “Maigida don Allah manta da shi, ci gaba da duka na.”

Daga Isah Ramin Hudu Hadeja, 08060353382

 

Karya doka

Dan sanda ne ya kama wani Koje yana fitsari a daidai allon da aka rubuta cewa: “Laifi ne a yi fitsari a nan. Duk wanda aka kama, zai biya tarar Naira 500.” Dan sanda: “Me ya sa kake fitsari a nan, ba ka ga allon nan ba?” Koje: “Don Allah ka yi hakuri!” Dan sanda: “Sai ka biya tarar Naira 500 ko in tafi da kai.” Koje: “To ga Naira dubu daya, sai ka ba ni canji.” Dan sanda: “Ba ni da canji, kara yin fitsarin sau daya a madadin canjinka.”

Daga Bashir Yahuza Malumfashi, 08065576011

 

Direba da ustaz

Wani direba ne ya kira wani ustaz domin su tafi aikin mota tare. Sun fita tun safe suna aiki har rana ta yi zafi. Bayan an cika mota da fasinja sai ustaz ya ce su kawo kudin mota. Da aka fara bashi kudin, sai ya shafa aljihu domin ya ba wani mutum canji sai ya ji babu kudin da suka yini suna aiki a aljihun, wani ya sace. Nan da nan sai ya fara kabbara da karfi, ya ce: “Allahu akbar, wani ya cuci kansa!” Direba ya juyo ya ce: “Ustaz, yaya aka yi ne?” Shi kuwa ya ce: “Ai duk cinikin da muka yi yau, wani ya sace su.” Direba ya ce: “Ka ce ya cuci kansa ko dai ya cuce mu?”

Daga Khalil Muhammad, 08031908918